Satar biliyan ta zama wasa?

Spread the love

ALI ABUBAKAR SADIQ

Idan ni alƙali ne aka kawo min ma’aikacin nan na NNPC da ake zargin satar biliyan 80, idan na tabbatar da laifinsa cewa ya saci biliyan 80 na talakawa, kun san wane hukunci zan yanke masa?

Kawai sai na yanke hukuncin cewa a kai shi gidansa a saka sojoji a ƙofar gidan a barshi cikin iyalinsa babu fita ko ƙofa, a kawo Naira biliyan ɗaya a ajiye masa ace kawai ya ƙirge su. Kun san idan zai kirga kowacce Naira ɗaya a sakan guda, sai ya ɗauki shekaru 31 da wata bakwai yana ƙirgawa? Wannan shine babu abinda ya ke yi sai ƙirgar. To a barshi ya yi barci, sallah da cin abinci duk sanda ya ke bukata. A haka shekaru nawa zai ɗauka kenan? Tabbas zai ninka waɗannan shekaru.

To idan kuwa za a ce ya ƙirga wannan biliyan 80 da ƙwandala-ƙwandala, sai ya yi shekaru 2,536 kafin ya ƙirge su jama’a.

To yawan biliyan fa kenan, amma yanzu ana sace ta kamar shakar iska. Ba dole mutane su shiga talauci ba.

Kun san idan ka na da Biliyan ɗaya, a kullum za ka kashe miliyan biyu da dubu ɗari bakwai kenan a shekara. To shi wannan da ake zargin ya saci biliyan 80, idan a kullum din zai rika kashe miliyan biyu da dubu ɗari bakwai, sai ya yi shekara 80 ya na kashewa ba su ƙare ba.

Wato dai ina kyautata zaton ciwon nan na Kleptomania, wato ciwon sata, shine ya zama ciwon annoba da ke ta watsuwa tsakanin mutanen Nijeriya. Ciwon ya zama annoba, ba musulmi ba Kirista, ba ɗan Kudu ko ɗan Arewa. Ciwon sata ya shiga jinin ma’aikatan gwamnati da ƴan siyasa. Abin takaici sai ka ga wanda ya saci irin waɗannan kuɗaɗen, saboda dama Allah ba ya sonsa, sai kaga ba ya iya wani aikin alheri da su ballantana ya tsammaci wata sa’ida daga ubangiji. Ba ya taimakon ƴan uwa ballantana maƙwabta, ko al’umma. Duk inda za ka ga su na kashe kuɗi a hanyoyin riya ne da ashararanci. Ko kasuwanci wanda zai haɓaka tattalin arzikinsu da na al’umma ba za ka gan su a ciki ba, saboda Allah na musu mummunan tanadi sakamakon mugun halinsu.

Abin takaici shine al’umma ta raja’a ga bautar kuɗi, duk wani zati na ubangiji an mayar da shi kan kuɗi. Ina kyautata zato a ranar lahira, lokacin da Allah zai ware layukan bautar waninsa, kama daga layin masu bautar mala’iku, annabawa, sahabbai, Ahlul baiti, waliyyai, al’ada, ya’ya da bautar kai, to layin masu bautar kuɗi zai kwashi mutanen zamanina da dama.

Allah ya ba mu ikon kaucewa faɗawa duk wata bautar da ba ta Allah ba.

By ukarofi