
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya ce, Gwamnatin Tarayya ta shirya kammala aikin titin jirgin ƙasa mai tsawon kilomita 284, wanda ake ginawa a Kano – Jigawa – Katsina – Maraɗi, zuwa nan da shekarar 2026.
Ya bayyana hakan ne a Jihar Katsina, a lokacin da ya ke ƙaddamar da Cibiyar Harkokin Noma ta Katsina da kuma titin yanke mai tsawon kilomita 24 dake yankin Tashar Bala a jihar.
Shugaba Tinubu ya ce, titin jirgin, wanda ya kama daga Kano zuwa Maraɗi a ƙasar Nijar, zai taimaka wajen sauƙaƙe harkokin sufuri ga mutane da kayayyakin kasuwanci a shiyyar Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Ya kuma ce, sun bada kwangilolin gyaran titunan Mararraban Ƙanƙara – Dutsinma – Katsina da na Zariya zuwa Hunƙuyi zuwa Dabai da kuma na Ƙafur zuwa Malumfashi zuwa Dayi da gidan Mutum Ɗaya.
Ya ƙara da cewa, a yanzu ana cigaba da zango na biyu na aikin titin Katsina biyo bayan da Gwamnatin Tarayya ta warware matsalolin da suka haifar da cikas a baya.
