Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa ƙaruwar ɓarnar da ake tafkawa a kan muhimman na’urorin wutar lantarki ya kawo cikas wajen cimma burin samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 6,000 zuwa Disambar 2024.
Ya bayyana cewa, gwamnati ta aiwatar da matakan kaiwa ga gaci kuma tana kan hanya har sai da wasu zauna gari banza suka fara barnatar da wayoyin wutar lantarki, wanda hakan ya kawo cikas ga shirin.
Mai ba da shawara na musamman kan dabarun sadarwa da hulɗa da manema labarai, Bolaji Tunji ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Sunday PUNCH, lokacin da aka tambaye shi dalilan da suka sa aka kasa samar da tsayayyen wutar lantarki.
Samar da wutar lantarki a Nijeriya a halin yanzu yana tsakanin ƙarfin MW 4,000 zuwa 4,900 MW daga tashoshin samar da wutar lantarki 19, wanda ke aikin samar wa mutane miliyan 200 lantarki.
Misali, rahoton aiki na baya-bayan nan ya nuna cewa samar da wutar lantarki a ƙasar ya kai 4,363.79MW ya zuwa yau.
A farkon wannan shekarar, Adelabu ya yi alƙawarin samar da wutar lantarki a Nijeriya zai kai megawatt 6,000 a karshen shekara, inda ya ce an samu ci gaba a fannin a shekarar da ta gabata.
Sai dai kuma yawan latsewar wutar lantarki da ake samu a ƙasar akai-akai da ɓarnata hasumiyai daga ƙarshe ya yi illa ga wutar lantarkin, lamarin da ke kawo cikas ga yunƙurin bunkasa wutar lantarki a ƙasar.
Mashawarcin na musamman wanda ya bayyana ƙwarin gwiwar cimma wannan manufa a wata ganawa da ‘yan jarida a watan Nuwamba, ya bayyana cewa an ƙara kusan megawatt 1,000 tun bayan hawan gwamnati mai ci.
