Sau 41 aka kai wa ofisoshin INEC hari cikin shekara 2 — Yakubu

Daga AISHA ASAS

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa an kai wa kadarorin hukumar hari har sau 41 a sassa daban-daban na ƙasar nan a cikin shekara biyu da ta gabata.

Yakubu ya faɗi haka ne a taron gaggawa da hukumar ta yi da hukumomin tsaro ƙarƙashin Kwamitin Tuntuɓa kan Tsaron Harkar Zaɓe, wato ‘Inter-agency Consultative Committee on Election Security’ (ICCES).

Yakubu ya ce ya kamata daga yanzu a ɗau hare-haren da ake kai wa kadarorin hukumar a matsayin babban abin damuwa ga ƙasa baki ɗaya.

Ya ce, “Ba shakka, makwannin da su ka gabata sun kasance babbar matsala ga wannan hukuma. Yawan ƙone-ƙone da lalata kayan hukumar da ake yi ya zama babbar barazana ga ayyukan da mu ka tsara gudanarwa da ma aikin shirya zaɓe baki ɗayan sa.

“A cikin shekaru biyu da su ka gabata, hukumar ta lissafa jimillar hare-hare guda 41 da aka kai wa kadarorin ta. Tara daga cikin waɗannan hare-haren sun auku ne a cikin shekarar 2019, sai kuma guda 21 a cikin 2020.

“A cikin makwanni huɗu da su ka gabata kuma, ofisoshi 11 na hukumar ko dai an banka masu wuta ko kuma an lalata su. Biyu daga cikin su ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga daɗi ne su ka kai masu hari, yayin da ‘yan iskan gari su ka kai sauran hare-hare 10 a lokacin zaɓe da rikicin bayan zaɓe.

“Amma dai yawancin hare-haren (29 daga cikin 41) ba su da nasaba da batun zaɓe ko ayyukan zaɓe.

“A gaskiya, 18 daga cikin su sun faru ne a lokacin zanga-zangar nan ta #EndSARS da aka yi a Oktoba na bara yayin da hare-hare 11 wasu ”yan bindigar da ba a sani ba’ da ”yan iskan gari’ ne su ka aikata su.”

Shugaban ya ce duk da yake hukumar ta na ƙoƙarin gano yawan asarar dukiyar da ta yi a lokacin hare-haren kwanan nan, binciken ta na farko-farko ya zuwa yanzu ya nuna cewa ta yi asarar akwatunan zaɓe 1,105, rumfunan zaɓe 694, janareton bada wutar lantarki 429 da kuma motoci 13 (ƙirar Toyota Hilux).

Ya ce ta hanyar yin aiki tare da hukumomin tsaro, INEC za ta iya tsaida waɗannan hare-haren da ɓarnata kayan zaɓe da ake yi mata.

“Waɗannan hare-haren, waɗanda da farko sun yi kama da ɗaiɗaikun al’amura da kan faru jefi-jefi, yanzu sun zama masu aukuwa a kai a kai kuma shiryayyu, kuma ana yin su ne domin a karya lagon babban tsarin da ake yi na gudanar da zaɓuɓɓuka a ƙasar nan.

“Hakan zai yi wa ƙarfin hukumar na shirya zaɓuɓɓuka da sauran ayyukan zaɓe zagon ƙasa, sannan ya rusa tsarin zaɓe da na dimokiraɗiyyar ƙasar nan.

“Ba shakka, waɗannan hare-hare kan kadarorin hukumar ya kamata daga yanzu a kalle su a matsayin babbar matsalar tsaro da ta shafi ƙasa baki ɗaya.”

Shugaban na INEC ya nanata buƙatar da ke akwai ta ƙarfafa ayyukan kwamitin ICCES domin a rage waɗannan ayyukan ta’asa waɗanda ba su da wani hurumi.

Ya ce, “Hakan ba kawai zai tsaya ga yin amfani da ƙarfin mu na ɗai ɗaya ko na haɗaka a cikin ICCES ba, zai buƙaci haɗin gwiwa da jama’a da garuruwa da dukkan masu ruwa da tsaki a al’amarin.”

Yakubu ya kuma nuna buƙatar da ke akwai ta kwamitin ya yi amfani da kayayyakin INEC da agajin garuruwan da ofisoshin hukumar su ke wajen gano maganin matsalar da ake ciki.

Ya ce a matsayin ta na hukuma, INEC ta na yin nata binciken na cikin gida domin nemo amsoshi.

Ya tuno da cewa INEC ta yi zama da Zaunannun Kwamishinonin Zaɓe (REC) da ta ke da su a makon da ya gabata inda ta karɓi bayanai daga wajen su kan barazanar da ke wanzuwa.

Ya ce, “A yanzu haka mu na tattara shawarwari masu amfani da aka samu daga wajen taron da sauran binciken cikin gida, waɗanda mu ke fatan za mu miƙa wa wannan kwamitin a nan gaba kaɗan.

“Na fahimci cewa hukumomin tsaro su na yin nasu binciken.

“Ban da tsaron Ranar Zaɓe, mu na duba yiwuwar samar da wani tsari na tsare kayan zaɓe a duk tsawon shekara kuma ta kowane ɓangare a ƙarƙashin kwamitin na ICCES.”

Yakubu ya yi fatan cewa taron na ICCES zai kasance mataki na farko wajen gano nagartaccen maganin matsalolin da ake fuskanta. Ya ƙara da cewa rusa tsarin zaɓe daidai ya ke da yi wa dimokiraɗiyyar mu zagon ƙasa da kuma tada hankalin ƙasa.

A nasa jawabin, mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan tsaron ƙasa (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno (ritaya), wanda kuma shi ne shugaba na biyu na kwamitin na ICCES, ya ce ofishin sa ya na aiki tare da sauran hukumomi domin su haɗa gwiwa da INEC su kare martabar dimokiraɗiyyar Nijeriya da kuma buƙatar jama’ar ƙasa.

Ya ce, “A matsayin mu na ‘yan Nijeriya, lallai mun ga abubuwa da dama da ke faruwa kuma mun haɗu da abubuwa marasa daɗi, waɗanda su ka shafi tsarin zaɓe, abubuwan da masu aikata laifi ke yi, waɗanda su ka dage wajen ganin sun ɓata wannan tsarin wanda ya kamata a ce tsarkakke ne, bayyananne, kuma a bar su zaɓa wa kan su abin da su ke so.

“Gaskiya ne, mun taru a nan ne domin mu duba hanyoyi da buƙatu na tsaida wannan ƙaruwar aikata laifin da of quickly stopping the rising hare-hare da lalata dukiya a matsayin aikin ƙasa baki ɗaya.

“Gaskiya ne, a ko yaushe Ofishin NSA ya kasance ya na aiki sosai kuma wurjanjan ba tare da gajiyawa ba wajen mara wa ayyukan INEC baya, da kuma jami’an gwamnati waɗanda doka ta ɗora wa alhakin yaƙar duk wani abu da zai rusa abin da aka faro shi daga 1999.

“A shirye mu ke mu tabbatar da cewa an kare muradin jama’a, ko da kuwa me ya faru, ko da kuwa me wani mutum ke so, babu dalili kamar yadda masu karya doka ke so ta hanyar duƙufa wajen ɓata wannan ƙoƙarin.

“Ina fatan abin da aka zartar a wannan taron zai amfanar sosai.

“Ya kamata mu samu cigaba wajen ganin mun aiwatar da dukkan abin da zai faranta ran tsarin zamantakewar mu.”

NSA ya yi kira ga dukkan shugabannin hukumomin tsaro da su inganta aikin ma’aikatan su da ke mara wa wannan tsari baya.

Shi ma mai riƙe da muƙamin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Alhaji Usman Baba, ya bada tabbacin cewa a shirye ‘yan sanda su ke su jagoranci aikin tsaro a lokutan zaɓe tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.

Haka kuma ya yi alƙawarin cewa rundunonin ‘yan sanda na jihohi za su yi aiki tare da kwamishinonin zaɓe (RECs) domin maimaita tsarin bada tsaron don yin zaɓe cikin lumana.

Baba ya ce shirin da INEC ta yi don gudanar da wani zaɓe, idan har babu isasshen shirin tsaron kafin zaɓe da lokacin zaɓen da bayan zaɓen, ba zai yi nasara ba.