Sau uku babban layin wutar lantarki na ƙasa na ɗaukewa ƙasa da makonni biyu

Spread the love

Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya sake ɗaukewa wanda hakan ya yi sanadiyar jefa sassan ƙasa cikin duhu.

Wannan shi ne karo uku a ƙasa da makonni biyu da babban layin lantarkin ya ɗauke, don kuwa irin haka ya faru sau biyu kimanin mako guda da ya gabata.

A cewar masu kula da cibiyar lantarki ta ƙasa, a ranar Talata aka samu koma bayan ƙarfin wutar lantarkin da ake samarwa daga megawat 3,594.60 zuwa megawat 42.7.

Sun ce ya zuwa lokacin da lamarin ya faru, cibiyar lantarki da ke Delta kaɗai ke da wuta mai ƙarfin megawat 41.00, yayin da cibiyar da ke Afam ke da megawat 1.7.

Wannan na zuwa ne kwanaki biyar bayan da layin ya ɗauke sau biyu wanda hakan ya yi sanadiyar jefa ƙasa cikin duhu.

Idan za a iya tunawa a ranar Alhamis da ta gabata aka maido da wutar lantarki a faɗin ƙasa bayan wasu awanni da ɗaukewarta sakamakon ɗaukewar da cibiyar lantarki da ke Osogbo a Jihar Osun ta yi.

By Editor