Saudiyya ta tallafa wa ‘yan gudun hijira da abinci a Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Ƙasar Saudiyya ta bada tallafin kayan abinci na kuɗi Dalal bilyan $1.1 domin raba wa ‘yan gudun hijira a jihar Barno da Yobe da Zamfara.

Da yake jawabi a wajen taron ƙaddamar da rabon kayayyakin a Talatar da ta gabata a birnin Maiduguri, Mataimakin Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Ibraheem Alghamedi, ya ce Sarki Salman ya ɗauki wannan matakin ne domin ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Jakadan ya ce, “Ina mai amfani da wannan dama wajen jaddada kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Masarautar Saudiyya da Tarayyar Nijeriya.

“Haƙika Saudiyya ta ƙuduri aniyar bunƙasawa da kuma kyautata wannan alaƙa ta kowane fanni.”

Alghamedi ya ƙara da cewa, “Saudiyya ta ɗauri aniyar raba tallafin abinci ga ƙasashen duniya ciki har da Nijeriya, ba tare da la’akari da wani bambancin addini ko ƙabila ba.”

Jami’in ya nuna cewa ko a 2018 ƙasarsa ta bada makamancin wannan tallafi inda ta turo kayayyaki na kuɗi Dala milyan $10 zuwa shiyyar Arewa-maso-gabas. Kana a 2019 ta bada tallafi a ɓangaren kiwon lafiya ga jihar Oyo da Nasarawa.

Ya ce Saudiyya na da niyar bada gudunmawa ga fannin lafiya a Kano da Bauchi inda take harin mutum 50,000 su ci gajiyar shirin. Yana mai cewa, shirin zai faɗaɗa har zuwa yankunan Kudu-maso-kudu da Kadu-maso-gabas na Nijeriya.

Kazalika, ya ce Saudiyya ta tallafa wa Nijeriya da kayan aiki na kimanin Dala milyan guda don yaƙi da annobar korona a ƙasar.

Sa’ilin da take karɓar tallafin, Ministar Jin Ƙai, Agaji da Kyautata Rayuwar ‘Yan Ƙasa, Sadiya Farouq, ta yaba da ƙoƙarin Saudiyya, tare da bada tabbacin Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da ta jihar Barno (SEMA) za su kula da rabon kayayyakin ga waɗanda aka yi domin su.

Tallafin abincin da Saudiyya ta bayar ya haɗa da wake, shinkafa, gishiri, magi, man girki, tumatiri da sauransu.

A madadin Gwamnatin Jihar Barno, Shugabar hukumar SEMA, Hajiya Yabawa Kolo, ta jinjina wa Saudiyya bisa irin gudunmawar da ta saba bai wa Nijeriya. Ta ce tallafin ya zo a daidai lokacin da ake da buƙatarsa a wannan wata na Ramadan.

Fatima Hassan da Falmata Bukar da Ali Musa da Mustafa Alimami na daga cikin ‘yan gudun hijirar da suka amfana da tallafin. Baki ɗayansu sun yi ra’ayin cewa tallafin zai taimaka musu da ahalinsu musamman ma a wannan lokaci na azumi.