Naɗa ɗan marigayi Deby matsayin shugaban Chadi ya bar baya da ƙura

Spread the love

Daga UMAR M. GOMBE

‘Yan hamayya a siyasar ƙasar Chadi sun ƙi amincewa da naɗin da sojojin ƙasar suka yi wa ɗan tsohon shugaban ƙasar, marigayi Idriss Deby a matsayin sabon shugaban riƙo na ƙasar.

Sojoji sun naɗa Muhammat Kaka Idriss Deby a matsayin shugaban riƙo na ƙasar ne biyo bayan rasuwar mahaifinsa a Talatar da ta gabata.

Sai dai da alama naɗin bai yi wa wasu ‘yan ƙasar daɗi ba inda wasu ‘yan siyasa masu hamayya suka fito suka nuna rashin amincewarsu game da naɗin tare da cewa ƙasar ba ta mulkin kama-karya ba ce.

Kafin wannan lokaci, General Kaka kamar yadda aka fi saninsa da shi, shi ne mai kula da tsaron shugaban ƙasa. Kuma an naɗa shi don kula da ƙasar ne na watanni 18 masu zuwa inda ake sa ran gudanar da zaɓe.

Sai dai masu fashin baƙi a sassan duniya na ganin matakin da sojojin suka ɗauka bai dace ba, sun ce kamata ya yi shugaban majalisar ƙasar ya karɓi ragamar mulkin ƙasa idan ya zamana shugaba mai ci ya cim ma ajalisa har zuwa lokacin da za a gudanar da zaɓe.

A halin da ake ciki, an bada sanarwar rushe tsohuwar gwamnatin ƙasar da ma majalisarta, an sanya dokar hana zirga-zirga sannan an rufe iyakokin ƙasar.

Da ma dai an yi hasashen cewa mutuwar tsohon shugaban ƙasa ka iya haifar da rikicin siyasa a ƙasar.

Rahotanni daga ƙasar sun nuna cewa an girke tankokin yaƙi a fadar shugaban ƙasar inda suke ci gaba da zaman ko-ta-kwana.

By Editor