
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙasar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa mafi yawa cikin sama da shekaru 30 akan fursunoni 198 a ranar Asabar, kamar yadda ƙididdiga ta AFP ta nuna.
Wannan ya nuna ƙasar ita ce ta uku a zartar da hukuncin kisa kan fursunoni da adadi mafi yawa bayan ƙasashen Chana da Iran a shekarar 2023 kamar yadda ƙungiyar ‘Amnesty International’ ta bayyana.
Haka nan, ƙungiyar ta ce adadin ya wuce na shekarun 2022 da 1995 inda aka samu 196 da kuma 192.
Amnesty International ta fara aikin tattara bayanai game hakan ne tun a shekarar 1990.
