Nijeriya na asarar Dala Biliyan ɗaya duk wata ga masu fita neman lafiya ƙasashen waje

Spread the love

Bankin Raya Afirka ya bayyana cewa Afirka tana rasa dala tiriliyan 2.4 duk shekara ta fuskar tattalin arziki saboda rashin zuba jari a ɓangaren lafiya, inda Nijeriya ke rasa dala biliyan ɗaya duk wata saboda rashin haramta yawon neman lafiya a ƙasashen waje.

AFDB ya tabbatar wa gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, cewa zai taimaka masa wajen haɓaka tattalin arzikin jihar zuwa tattalin arzikin ƙarni na 21, ta hanyar bunƙasa ɓangaren kiwon lafiya a jihar da kuma taimaka wa Nijeriya wajen tsare dala biliyan ɗaya da ake asara duk wata saboda rashin haramta yawon neman lafiya a ƙasashen waje.

Shugaban tawagar AfDB zuwa Nijeriya, Mista Babatunde Omilani, ya bayyana hakan yayin ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Legas a ranar Jumma’a. Ya ce tawagarsa ta shafe kwanaki 10 a Legas suna nazarin ɓangaren kiwon lafiya na jihar, kuma tawagar ta ziyarci dukkan cibiyoyin kiwon lafiya na jihar don gano wane irin gudunmuwa za su bayar.

“Mun yi cikakken nazari tare da Hukumar Lafiya ta Duniya, inda muka gano cewa Afirka tana rasa dala tiriliyan 2.4 duk shekara saboda rashin zuba jari a kiwon lafiya.

A cikin jawabinsa gwamnan ya gode wa ƙoƙarin AfDB kuma ya roƙi su cika wannan alkawura, kuma su sanar da jihar irin gudunmawar da za ta bayar don cimma wannan manufa. Ya ce, “Muna da yaƙinin jagorancin bankinku. Muna da yaƙinin cewa shugabancin yana da tsari, shi yasa kuka zo nan, kuma muna farin cikin da kuka yi amfani da Legas a matsayin gwaji. Muna son tabbatar muku cewa tabbas a shirye muke domin ganin hakan ya samu nasara.

By ukarofi