Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi ta nemi agaji don tallafawa al’ummomin da ambaliyar bana ta lalatawa matsugunai da kuma gonaki.
Kwamishinan yaɗa labarai Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi ne ya bayyana haka ranar Juma’ar da ta gabata lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ofishinsa.
Kwamishinan ya bayyana cewa kimanin gidaje 328,000 ne suka rushe yayin da gonakin abinci da suka hada da gero, shinkafa, wake, masara, gyada da dai sauransu da yawansu ya kai hekta 858, 000 ruwan ya mamaye.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Jihar Kebbi tana neman agaji don tallafawa ga waɗanda iftila’in ambaliyar ruwan ya yi wa ta’adi saboda duk da ya ke tana nan tana iya ƙoƙarin ta na ganin ta inganta yanayin da su ke ciki.
Yanzu haka dai wannan gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Malam Nasir Idris tana nan tana shiga lungu da saƙo don tabbatar da duk wanda abin ya shafa an zayyana sunansa da kuma irin hasarar da ya yi don miƙawa ga hukumomin da abin ya shafa musamman daga gwamnatin tarayya.
Gwamnatin jihar ta Kebbi tana neman agajin cikin gaggawa don tanadar wuraren zama da abinci saboda yanzu haka dubban mutane sun rasa matsugunai da dukiyoyi mai tarin yawa da suka sami kawunansu cikin wani yanayi na damuwar rashin abinci da kayan amfanin yau da kullum.
Kwamishinan na yaɗa labarai ya yi ƙarin haske dangane da batun naira billiyan uku da aka ce gwamnatin tarayya ta baiwa jihar don tallafawa waɗanda ambaliyar ruwan ta shafa inda ya ce “Ba ni da masaniya ko ku kuɗaɗe sun shigo hannun gwamnatin Jihar Kebbi” sai dai ta nuna rashin gamsuwarsa bisa ga yadda waɗansu yan majalisun tarayya suka yi ko-oho da
al’ummar da wannan abin ya shafa ballantana su yi ƙoƙarin kawo agaji.
Ya bayyana cewa a ɗaya ɓangaren, gwamnatin jihar Kebbi ta sha alwashin samar da iri na nau’o’in abinci dabam-daban ga manoma don cigaba da noma, haka-zalika za ta ɗauki duk matakin da ya dace don ganin ta tayarda mutanen da ke zaune a wurare masu hatsari don canja musu wajen zama.
Wata yar ƙaramar ƙididdiga ta bayyana cewa an sami rahotannin mutuwar mutum bakwai daga ƙaramar hukumar Nyaski, takwas daga ƙaramar hukumar ta Maiyama, biyar daga ƙaramar hukuma ta Kalgo, bakwai daga ƙaramar hukuma ta Jega sai kuma biyu cikin garin Birnin Kebbi sanadiyyar ambaliyar ruwan sama.
