
Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Jam’iyyun siyasa tara a Jihar Kaduna, sun zargi Abdul Ahmed Ishak, mashawarcin Gwamna Uba Sani na musamman kan hulɗa da masu-ruwa-da-tsaki, da yin awon gaba da kuɗaɗen zaɓen da aka tanada don samar da adalci a tsakanin dukkan jam’iyyu.
Jam’iyyun da suka haɗa da; PRP, YPP, LP, NNPP, PDP, AAC, AA, ZLP da BP sun yi wannan zargin ne a wata sanarwar haɗin-gwiwa da suka raba wa manema labarai a Kaduna.
“Wannan cin amana ne ga ƙudirin Gwamna na yin gaskiya da riƙon amana. Muna buƙatar a yi bincike cikin gaggawa tare da gyara.”
Sanarwar ta kuma ce, “wannan karimci na Gwamna Uba Sani wata shaida ce ta sha’awarsa na gudanar da zaɓe wanda zai bai wa dukkan jam’iyyu damar fafatawa a tsakanin su”, inji sanarwar.
Jami’iyyun sun buƙaci Gwamna Uba Sani da; Zama da shugabannin jam’iyyu: Zaman tattaunawa da dukkan jami’iyyun siyasa a jihar don magance matsalar kai tsaye.
- Bincike da gyara: Gaggauta binciken ayyukan Ishak da kuma maido da Babban Mataimaki na Musamman akan harkar jam’iyyu don sa-ido kan rabon kuɗaɗe cikin adalci.
- Hana faruwar matsalar a gaba: Kafa wani kwamitin da zai sa-ido kan ayyukan don hana faruwar irin wannan matsala.
- Tsawaita wa’adin KAD-SIECOM: Ba da ƙarin lokaci don bai wa ƴan takara samun cikakken shiri.
