
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A yunƙurinta na tabbatar da adalci ga manoma da makiyaya a gwamnatin Jihar Katsina ta bada umarnin buɗe duk wani Burtali ko wurin kiwo da aka rufe ba bisa ka’ida ba.
Umarnin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafe ne daga Fulani makiyaya akan yadda manoma ke datse hanyoyin kiwo da mashayar dabbobinsu ta hanyar nome wuraren.
Akan haka ne Gwamnan jihar, Dikko Raɗɗa ya umarci Sakataren gwamnatin, Abdullahi Garba Faskari ya ziyarci ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa don warware matsalolin.
Ƙananan hukumomin sune; Kaita, Mashi, Zango, Mai-Adua da Dutsinma inda a lokacin da ya kai ziyara, Abdullahi Faskari ya bayyana wa al’ummar yankunan cewa, gwamnati ba za ta yi sakaci da batun Fulani da makiyaya ba domin matsala ce da ta shafi tsaro a jihar.
Ya ce wannan dalili ya sa, Gwamna Raɗɗa ya bada umarnin cikin gaggawa don ganin an bi ƙa’ida a wuraren da aka samu irin matsalar.
Tuni sakataren da tawagarsa suka ziyarci Muludu a Mai-Adua, Dajin Ƴan Hakum, da dajin Babbar Gona duk a ƙaramar hukumar.
“Haka kuma mun ziyarci kauyen Rindi a ƙofar Kudu, ƙaramar hukumar Zango da kuma da ‘Atakar Grazing Reserve’ a ƙaramar hukumar Mashi”, inji sakatarensa.
Sauran wuraren da suka ziyarta sun haɗa da; Duba Grazing Reserve na Ƴanhoho a Kaita da Dajin Jaudi a Dutsinma.
Kafin ziyarar, Sakataren ya ce, sun zauna da ƙungiyoyin manoma da Fulani da sauran hukumomin da abin ya shafa inda aka tattauna hanyoyin warware matsalolin.
