Jami’an tsaro sun ceto manoma shida daga hannun ƴan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jami’an tsaro sun ceto manoman da ƴan bindiga suka sace a lokacin da su ke girbin masara a gonarsu dake ƙauyen Gurbin Magajiya a ƙaramar hukumar Jibiya.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Dakta Nasiru Mu’azu Ɗan-Musa ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce jami’an ƴan sintiri da aka fi sani da ƴan banga suka ankarar da sauran jami’an tsaro na al’umma da ƴan sanda, sojoji da da jami’an tsaro na farin kaya (DSS) waɗanda suka afka cikin dajin da aka ce an boye manoman.

Kwamishinan ya ce an ceto su kuma su na cikin ƙoshin lafiya inda nan ba da jimawa ba za a miƙa su ga iyalansu.

Ya kuma yaba da namijin ƙoƙarin da jami’an tsaron suka yi wajen ceto manoman ba tare da wani ya samu ko da ƙwarzane ba.

Ɗan-Musa ya jaddada ƙudirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na kakkaɓe ƴan ta’adda tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.

By Babaji