Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Attajirin ɗan kasuwa kuma Shugaban Kamfanin First HoldCo Plc, Femi Otedola, ya yaba da sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar, yana mai cewa matakan sun sanya tattalin arzikin Nijeriya kan turbar samun ci gaba mai ɗorewa.
Otedola ya bayyana hakan ne a birnin Paris na ƙasar Faransa ranar Litinin, bayan wata liyafar cin abinci ta sirri da ya
halarta tare da Shugaba Tinubu, wanda ke Turai domin hutun aiki.
Ya ce sauye-sauyen da Tinubu ya aiwatar, waɗanda ya bayyana a matsayin matakai “masu ƙarfin hali da hangen nesa”, sun sanya tattalin arzikin ƙasar kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa.
Otedola ya ce alamun sakamakon waɗannan sauye-sauye na ƙara bayyana, inda ya kawo misalin shigar wasu manyan kamfanonin Nijeriya cikin FTSE Russell Frontier 50 Indeɗ, da yadda kasuwar hannayen jari ta Nijeriya, NGɗ, ta kai matsayi na tarihi, tare da ƙarin jarin waje kai tsaye da kuma farfaɗowar kwarin gwiwar masu zuba jari.
Ya kuma ce an samu ci gaba wajen samar da haɗaɗɗiyar kasuwar canjin kuɗaɗen waje, yayin da ajiyar kuɗaɗen waje ta ƙasar ta kai kusan dala biliyan 55.
Otedola ya ce waɗannan abubuwa na daga cikin alamun da ke nuna sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar suna haifar da sauye-sauye a sassa daban-daban na tattalin arzikin ƙasar.
Tun bayan da Tinubu ya karɗi mulki a watan Mayun 2023, Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da wasu sauye-sauye da nufin farfaɗo da tattalin arziki, bunƙasa ci gaba da kuma ƙarfafa daidaiton tattalin arzikin ƙasar.
Daga cikin manyan matakan akwai cire tallafin man fetur, wanda a baya ke cinye tiriliyoyin naira daga baitulmalin gwamnati a duk shekara.
Matakin, duk da cewa ya jawo ƙarin tsadar rayuwa, ya samu karɗuwa a wajen wasu manazarta a matsayin wani mataki da zai iya taimakawa wajen jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje.
Gwamnati ta kuma sauya tsarin kasuwancin canjin kuɗaɗen waje, ta hanyar kawar da tsarin farashin canjin kuɗi daban-daban tare da mayar da shi zuwa tsarin da buƙata da wadata ke taka muhimmiyar rawa wajen ƙayyade darajar naira.
Hakan ya biyo bayan gagarumin sauyin darajar naira, matakin da gwamnati ta ce zai taimaka wajen jawo jarin waje, ko da yake ya ƙara matsin lambar hauhawar farashi.
A wani ci gaba, Nijeriya ta sake komawa cikin jerin ƙasashen Frontier Market na FTSE Russell, bayan shafe shekaru kusan uku tana cikin wani rukunin da ba a tantance kasuwarta ba.
Bayan wannan sauyi, wasu manyan kamfanonin Nijeriya ciki har da First HoldCo, ɗangote Cement, Zenith Bank, GTCO, MTN Nigeria da Aradel Holdings sun shiga cikin FTSE Frontier 50 Indeɗ a watan Satumban 2026. First HoldCo ta tabbatar da cewa shigar da ita cikin jerin ya fara aiki daga ranar 21 ga Satumba.
Shigar kamfanonin cikin jerin na ba su damar ƙara samun ganin idon masu zuba jari na ƙasashen waje, tare da samar da ƙarin dama ga masu zuba jari da ke neman saka kuɗi a kasuwannin Frontier.
A wani ci gaba makamancin haka, bayanan da Otedola ya ambata sun nuna cewa ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ta kai kusan dala biliyan 55, lamarin da ya ƙara daga cikin abubuwan da ya kawo a matsayin alamun ci gaba a tattalin arzikin ƙasar.
