Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Kwalejin Koyar da Ayyukan Lafiya da Kimiyyar Zamani ta Sahal College of Health Sciences and Technology (SCHST), Kano, ta gudanar da bikin yaye ɗalibai 75 da suka kammala karatunsu a fannoni daban-daban.
Daga cikin ɗaliban da aka yaye akwai ɗalibai 25 a fannin Basic Health Orientation da kuma ɗalibai 50 a fannin Basic Remedial Science.
An gudanar da bikin ne a harabar kwalejin da ke Kano a ranar Lahadin da ta gabata tare da halartar iyaye, malamai da sauran baƙi.
A jawabinsa na maraba, ɗaya daga cikin malaman kwalejin, Malam Hassan Magaji, ya yi kira ga iyaye da su ci gaba da ba ‘ya’yansu goyon baya ta hanyar samar musu da abubuwan da za su taimaka wajen ci gaban karatunsu.
Ya kuma taya ɗaliban murnar kammala wannan mataki na karatu tare da tunatar da su cewa hakan ba shi ne ƙarshen neman ilimi ba, illa wata dama ce ta ci gaba da neman ƙarin ilimi da ƙwarewa.
Da yake bayyana manufar shirya bikin, shugaban kwalejin, Malam Ibrahim Muhammad Alkanawi, wanda Dr. Abubakar Uba Magaji Magayaki ya wakilta, ya bayyana farin cikinsa da nasarar da ɗaliban suka samu.
Ya yabawa iyaye da suka jajirce wajen kula da karatun ‘ya’yansu tun daga farkon karatunsu har zuwa lokacin kammalawa.
A cewarsa, an shirya bikin ne domin taya ɗaliban murnar wannan nasara tare da jan hankalinsu kan muhimmancin ci gaba da neman ilimi da kuma amfani da ilimin da suka samu wajen yi wa al’umma hidima.
Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin ƙalubalen da makarantar ke fuskanta shi ne yadda wasu daga cikin iyaye ba su fahimci muhimmancin karatun fannin lafiya ba, lamarin da ke hana wasu matasa samun damar shiga wannan fanni.
Saboda haka ya yi kira ga iyaye su kasance masu ƙarfafa wa ‘ya’yansu gwiwa wajen neman ilimi, musamman a fannin kiwon lafiya wanda yake da matuƙar muhimmanci ga ci gaban al’umma.
Haka kuma ya yaba wa malamai da ma’aikatan kwalejin bisa ƙoƙarin da suke yi wajen koyarwa da tarbiyyar ɗalibai.
A yayin bikin, ɗaliban sun karrama shugaban kwalejin da wasu daga cikin malamansu da lambobin yabo domin nuna godiya da jin daɗinsu kan irin gudunmawar da suka bayar wajen koyar da su da kuma shiryar da su zuwa ga kyakkyawar makoma.
