Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Kungiyar Kare Haƙƙin Jama’a da Gaskiya ta SERAP ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, su bayyana yadda aka kashe Naira Biliyan 18.6 da aka ware domin gina ofishin Rukunun Ofisoshin Majalisar Aasa, kamar yadda rahoton mai binciken asusun gwamnati na 2022 ya nuna.
SERAP ta nemi shugabannin majalisun su bayyana sunan kamfanin da ya karɓi kuɗin, tare da bayyana cikakken bayani kan masu hannun jari, shugabanni da adireshinsa.
Kungiyar ta kuma buƙaci a yi bayani kan yadda aka karya dokar saye da kaya ta gwamnati (Procurement Act), saboda babu wata tantancewa ta buƙata, babu tallan gayyatar kamfanoni, kuma babu takardar amincewa daga hukumar BPP ko majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC).
A cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce bin diddigin lamarin zai tabbatar da cewa majalisar tana aiki ne don amfanin jama’a, ba don son kai ba.
SERAP ta bayyana cewa rahoton ofishin mai binciken asusun gwamnati da aka wallafa a ranar 9 ga Satumba, 2025, ya nuna cewa hukumar majalisar ta biya fiye da Naira biliyan 11.6 ga wani “kamfani marar suna” domin aikin gina rukunin cikin watanni 24.
Rahoton ya ƙara da cewa, an biya kuɗin ne a ranar 11 ga Agusta, 2020, amma daga baya aka gano cewa an ƙara farashin aikin da sama da Naira biliyan 6.9, inda aka sake biyan kuɗi a ranar 29 ga Nuwamba, 2023 don “canja rufin wurin zuwa ofisoshi”.
SERAP ta ce dukkanin kwangilolin an bayar da su ba tare da an yi binciken buƙata ba, babu tallan jarida, babu tsari na gasa tsakanin kamfanoni, babu kwangilar rubuce, kuma babu amincewa daga FEC ko takardar “no objection” daga hukumar BPP.
Mai binciken asusun gwamnati, a cewar rahoton, yana nuna damuwa cewa kuɗin Naira biliyan 18.6 da aka ware domin aikin na iya ɓacewa, kuma ya buƙaci a bayyana yadda aka yi da su.
SERAP ta ce lamarin na iya zama babban laifi na cin amanar jama’a, karya kundin tsarin mulki da kuma saɓa wa dokokin yaƙi da rashawa.
ƙungiyar ta bayyana cewa abin damuwa ne ganin yadda majalisar ta kasa nuna gaskiya da riƙon amana, tana kuma zargin cewa kuɗin na iya zama an karkatar da su ko an sace su gaba ɗaya.
SERAP ta buƙaci majalisar ta ɗauki mataki cikin kwanaki bakwai tun daga lokacin da ta karɓi wasikar, tare da gargaɗin cewa idan ba a yi abin da ya dace ba, za ta ɗauki matakin shari’a domin tilasta majalisar da hukumar su yi bayanin kuɗin.
Kungiyar ta kuma buƙaci a mika batun ga hukumomin yaki da cin hanci don bincike da gurfanarwa, sannan a dawo da kuɗin idan an gano sun ɓace.
A cewar SERAP, bayyana gaskiya game da kuɗin da kamfanin da ya karɓe su zai dawo da amincewar jama’a ga majalisar da kuma nuna cewa shugabannin ƙasar na da niyyar gaskiya, riƙon amana da bin doka.
