Barayi suka yi awon gaba da kayan sarautar Faransa mafi tsada daga gidan tarihi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wasu ɓarayi sun kai mummunan farmaki a gidan tarihin Louvre da ke birnin Paris, wanda shi ne mafi girma a duniya, inda suka sace kayan adon da ba a auna su da kuɗi, a cewar gwamnatin Faransa.

Rahotanni sun bayyana cewa ɓarayin sun yi amfani da motar crane wajen kakkarya tagar benen, suka shiga sashen da ke ajiye da kayan sarautar Faransa, sannan suka tsere a kan babura.

Ma’aikatar cikin gida ta ce, satar ta faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe a ranar Lahadi, daidai lokacin da gidan tarihin ya fara karɓar baƙi.

Ministar Al’adu Rachida Dati ta bayyana a kafar talabijin ta TF1 cewa satar ta ɗauki kusan minti huɗu kacal, inda ɓarayin suka nuna ƙwarewa ta musamman.

“Mun ga faifan bidiyo – ba su kai hari ga mutane ba. Sun shigo cikin nutsuwa, cikin minti huɗu sun fasa akwatunan gilashi, suka kwashe abin da suke nema suka gudu. Ba tare da tashin hankali ba — ƙwararru ne sosai,” inji ta.

Ta ƙara da cewa, an gano abin ado guda ɗaya a wajen gidan tarihin bayan ɓarayin sun tsere, wanda ake kyautata zaton kambin Sarauniyar Eugenie, matar Napoleon III ne, kuma an lalata shi a yayin satar.

Ministan cikin gida Laurent Nunez ya shaida wa France Inter cewa ɓarayin guda uku ko huɗu ne suka samu damar shiga ta hanyar crane da aka ɗora a kan mota.

“Sun fasa taga, suka nufi akwatunan ajiya da dama, suka sace kayan ado masu daraja da tarihi da ba a iya auna su da kuɗi,” inji shi.

Rundunar ‘yan sanda ta Faransa ta keɓe yankin gidan tarihin da titunan da ke kusa da shi bayan wannan mummunar sata, wadda ta tayar da hankali kan tsaron wannan fitaccen wurin tarihi.

Masu lura da harkokin al’adu sun dade suna gargaɗin cewa ana barin gidan tarihin Louɓre cikin matsin kuɗi, duk da cewa ya karɓi fiye da baƙi miliyan 8.7 a shekarar 2024.

An gina Louvre a shekarar 1546 a matsayin fadawar sarauta ta Sarki Francis I, kafin a maida shi gidan tarihi na jama’a a shekarar 1793 lokacin juyin juya halin Faransa. Yanzu haka yana ɗauke da sama da ayyukan fasaha 35,000, ciki har da shahararren zanen “Mona Lisa” na Leonardo da Vinci, kuma yana karɓar kusan baƙi dubu 30 a kowace rana.

By ukarofi