An ƙaddamar da sabon tsarin lasisin tuƙi na zamani a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta sanar da sabon tsarin lasisin tuƙi wanda ba zai an taɓa na’ura ba (contactless biometric system), wanda za a fara amfani da shi a faɗin ƙasar domin tabbatar da samun lasisi cikin sauri ba tare da jinkiri ko amfani da lasisin wucin-gadi ba.

Kwamandan hukumar, Shehu Mohammed, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin yayin ƙaddamar da yaƙin wayar da kai na “Ember Months 2025”, inda ya ce wannan tsarin sabon salo ne na sauya fasalin ayyukan FRSC gaba ɗaya zuwa tsarin fasahar zamani.

Ya bayyana cewa an riga an inganta cibiyoyin buga lasisi na hukumar domin su iya biyan buƙatun da suka taru kafin ƙarshen watan Nuwamba 2025. A cewarsa, wannan sabon tsari zai kawo ƙarshen jinkiri wajen fitar da lasisin dindindin.

“Yanzu tsarin ya zama mai sauƙi. Ba sai mutum ya danna yatsunsa a kan na’ura ba domin ɗaukar bayanai. Tsarin na amfani da fasaha wajen gane bayanan mai nema ta hanyar hoto da bincike kai tsaye cikin bayananmu na kwamfuta. Wannan tsarin mara taɓa-na’ura ne wanda zai sauya yadda muke gudanar da aiki,” inji Mohammed.

Ya ƙara da cewa, da zarar an gama ɗaukar bayanan mai nema, za a ba shi lasisin dindindin nan take ba tare da jiran mako biyu ko wata ɗaya ba.

Kwamandan ya tabbatar da cewa za a fara aiwatar da sabon tsarin cikin wannan watan, kuma zai haɗu kai tsaye da national database, domin tabbatar da sauƙin sabis ga kowa.

Dangane da tsaron hanya, Mohammed ya bayyana cewa an samu raguwar mace-mace a haɗurra idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Ya ce daga bayanan Operation Zero (15 ga Disamba 2024 zuwa 15 ga Janairu 2025), an samu mutuwar mutane 432 da raunuka 2,070 daga haɗurra 533. Amma daga Janairu zuwa Satumba 2025, an samu haɗurra 6,858 da suka yi sanadin mutuwar mutane 3,433 da raunuka 22,162 — abin da ke nuna ɗan ci gaba wajen rage haɗurra.

FRSC, a cewarsa, za ta ƙara ƙaimi wajen yaain wayar da kai musamman kan abubuwan da ke haddasa haɗurra kamar tuai cikin gajiya, ɗaukar kaya fiye da kima, da amfani da waya yayin tuƙi.

Haka kuma, Mohammed ya sanar da cewa hukumar za ta shirya Tarayyar Taron Afirka kan Mutanen da Haɗurra suka shafa daga 16 zuwa 18 ga Nuwamba 2025 tare da haɗin gwiwar KRSD Road Safety Foundation, domin aarfafa kula da waɗanda haɗurra suka rutsa da su bisa manufofin Majalisar ɗinkin Duniya na ‘Decade of Action for Road Safety’.

By ukarofi