Daga MAHDI MUSA MUHAMMMAD
Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su fi mayar da hankali wajen amfani da kayayyakin da ake samarwa a cikin ƙasa, a matsayin wata hanya ta ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasa da gina dogaro da kai.
Dangote ya bayyana haka ne yayin wata ziyara ga ‘yan jarida a matatar mai ta Dangote da ke yankin Lekki Free Trade Zone a Legas, ƙarƙashin jagorancin tsohon mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Reno Omokri, wanda kuma yake jagorantar ƙungiyar #GrowNairaBuyNaija — wacce ke yaƙi don bunƙasa sayen kayayyakin cikin gida.
Dangote ya ce, “Ina son in ƙarfafa dukkan ‘yan Nijeriya su riƙa sayen abin da aka yi a Nijeriya. Idan ka sayi kayayyakin cikin gida, kana taimaka wajen samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziai. Hanya ɗaya da za mu ƙarfafa ƙasar nan ita ce mu riƙa tallafawa kanmu.”
A nasa jawabin, Omokri ya bayyana matatar a matsayin cibiyar zamani ta duniya wacce fasaharta ta zarce na yau da kullum. “Matatar Dangote ba ta tsaya kan abin da ake kira zamani ba — ta nufi gaba. Ita ce makomar Nijeriya,” inji shi.
Ya bayyana cewa, tun bayan da matatar ta fara aiki shekara guda da ta gabata, tashar jiragen ruwa ta Dangote ta karɓi fiye da jiragen ruwa 650, inda kashi 60 cikin 100 na fitarwa ke zuwa Amurka, yayin da sauran ke zuwa Brazil, Argentina da wasu ƙasashe.
Matatar, wacce ke kan fili mai faɗin hektare 2,635, na da tankuna kusan 100, kowanne na iya ɗaukar lita miliyan 120. Daga kowace ganga ta man fetur da ake tacewa, ana fitar da kayayyaki fiye da 12 daban-daban.
Dangote Refinery kuma tana samar da man fetur da dizal masu daidaita da tsarin Euro 6, wanda ya fi ingancin man da ake amfani da shi a Turai, wanda hakan ke sa kayayyakin su dace da kowace kasuwa ta duniya.
Omokri ya jaddada cewa matatar tana da ma’aikata manya matasa da mata, inda kashi 60 cikin 100 na ma’aikatan dakin bincike na tsakiya (Central Laboratory) mata ne, ciki har da masana kimiyya na cikin gida da na ƙasashen waje.
Haka kuma matatar tana da ikon samar da wutar lantarki megawatt 500, yayin da masana’antar takin zamani da ke ƙarƙashinta ke ƙara megawatt 150, abin da ya kai kimanin kashi 10 cikin 100 na dukkan wutar lantarki da ake samarwa a Nijeriya.
Omokri ya bayyana ɗakin sarrafawa na matatar a matsayin “mai ban mamaki kamar duniyar fasaha,” saboda tsarin allon kwamfuta mai girman filin ƙwallon ƙafa wanda ke ba da damar ganin duk ayyuka a lokaci guda.
A nasa ɓangaren, mataimakin shugaban kamfanin Dangote, Deɓakumar Edwin, ya bayyana cewa matatar ta fuskanci yunƙurin ɓarna har sau 22 tun bayan da ta fara aiki.
Ya ce, “A wasu lokuta an yi ƙoƙarin kunna wuta ko buɗe bawul ɗin man don janyo matsala. Amma saboda tsarin zamani da muka tanada, tsarin tsaro da kashe gobara na mu kan gano kuma ya daƙile lamarin nan take.”
Edwin ya ƙaryata jita-jitar cewa matatar na fuskantar matsalar samar da ɗanyen mai ko aiki, yana mai cewa hakan “ba gaskiya ba ne,” kuma wani yunƙuri ne kawai da ake yi na ɓata suna ga nasarar da aka samu.
