Yaɗuwar labaran ƙarya a soshiyal midiya hatsari ne, dole a yi doka kan su – Sarkin Musulmi 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sanya doka kan amfani da kafafen sada zumunta saboda yaɗuwar labaran ƙarya da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Da yake jawabi a Babban Taron Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa a Birnin Kebbi, Sarkin ya ce mutane da dama na gaskata labaran da ba su da tushe a kafafen intanet, yana mai gargaɗin cewa lamarin na iya janyo tashin hankali.

Ya kuma yaba wa sojojin Nijeriya bisa ƙoƙarinsu wajen yaki da ‘yan ta’adda da ‘yan fashi, yana mai cewa suka da cin mutunci ga jami’an tsaro ba zai taimaka ba wajen kawo zaman lafiya.

A nasa jawabin, Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi, ya ce taken taron “ƙarfafa Haɗin Kan Al’umma Don Zaman Lafiya da Tsaro Mai ɗorewa” na nuni da buƙatar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma wajen magance matsalolin tsaro.

Taron ya samu halartar Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris da Ministan Tsare-Tsaren Kasafi da Tattalin Arziki da Etsu Nupe, da sauran manyan sarakuna daga Arewacin Nijeriya.

By ukarofi