Ba ni da niyyar koma wa APC – Gwamnan Osun

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana cewa ba shi da wani shirin koma wa jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa.

Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan taron farko na kwamitin karɓar baƙi na babban taron jam’iyyar PDP da ke tafe, wanda aka gudanar a Legacy House, Maitama, Abuja, Adeleke ya bayyana rikicin da ke cikin jam’iyyar PDP a matsayin lamari na cikin gida.

Ya ce, “Muna ganawa da kuma warware matsalolinmu a cikin gida. Wannan lamari ne na ‘yan uwa. Ba ma so wani daga waje ya zo ya ƙara masa sukari, barkono ko gishiri. Mu da kanmu muke kula da al’amuranmu. PDP gida ɗaya ce, kuma mun san yadda za mu tafiyar da harkokinmu.”

Gwamnan ya ƙara da cewa, “Mun kammala taron farko na kwamitin karɓar baƙi. Kowa ya halarta, kuma mun tattauna muhimman abubuwa da suka shafi nasarar babban taron jam’iyya domin komai ya tafi lafiya.”

Da yake magana kan sauyin sheƙa da ke faruwa, Adeleke ya ce ba ya cikin damuwa saboda kowane ɗan siyasa yana da ‘yancin yanke shawarar da yake so, amma hakan ba zai sauya komai a cikin PDP ba.

Ya ce, “Har yanzu muna da mambobi masu ƙarfi da goyon baya a faɗin ƙasar nan. Ba ni cikin damuwa.”

Adeleke ya kuma musanta jita-jitar da ake yadawa cewa yana shirin shiga APC saboda yana da abokai a cikin jam’iyyar.

Ya ce, “Ni mutum ne mai ilimi da wayewa. Idan ina da abokai a cikin APC, kuma suka gayyace ni zuwa biki ko wani taron zumunci, zan halarta. Amma hakan ba yana nufin cewa na koma jam’iyyarsu ba. A halin yanzu ni ne mataimakin shugaban kwamitin babban taronmu, wanda zai gudana a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, kuma ina nan a matsayin cikakken ɗan jam’iyyar PDP. Ni ne kuma shugaban kwamitin karɓar baƙi.”

By ukarofi