Yadda ’yan bindiga suka sace mutane 73 a wasu ƙauyuka biyu a Zamfara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

’Yan ta’adda sun yi awon gaba da mutum 73 ddaga ƙauyukan Buzugu da Rayau duk a ƙananan hukumomin Bukkuyum da ke jihar Zamfara.

Makamai Zagazola wanda ke wallafa Labaran hare-haren ‘yan ta’adda a shafinsa na sada zumunta da ke Intanet ya sanar da haka a shafinsa na ɗ ranar Litini da yamma.

Sanarwar ya nuna cewa maharan sun kai wa mazauna ƙauyukan hari ranar 18 ga Oktoba da misalin ƙarfe 2:45 na dare tare da yin garkuwa da mutanen ƙauyukan.

“Majiya da dama sun tabbatar cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike domin ceto mutanen sannan da dawo da zaman lafiya a ƙauyukan.

A farkon watan nan ne ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da mutane 30 a wani ƙauye da ke gundumar Zugu a ƙaramar hukumar Bukkuyum.

Kafin harin ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da kansiloli biyu da wani limami a wani ƙauye a ƙaramar hukumar Gusau.

A watan jiya, ‘yan ta’adda sun kashe mutum biyar a wani masallaci a ƙauyen Yandoto, ƙaramar hukumar Tsafe inda suka yi garkuwa da mutane da dama da ba a san adadinsu ba.

A cikin watan Agusta mahara sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu 100 inda a cikin su da mata da yara ƙanana da dama a Gamdum Mallam dake garin Adafka a ƙaramar hukumar Bukkuyum.

Sakamakon binciken da SBM ta gudanar kuma ta gabatar ya nuna cewa an yi garkuwa sa mutum 4,722 daga watan Yuli 2024 zuwa Yuni 2025 sannan an biya naira biliyan 2.57 kuɗin fansa a ƙasar nan.

Arewa maso Yamma ta zama matattarar yin garkuwa da kisan mutane a ƙasar nan inda jihar Zamfara ce jihar da ta fi fama da ayyukkan mahara a ƙasar nan.

By ukarofi