Cin hanci da rashawa ya yi ƙamari a hukumar NAHCON – Bin Uthman

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Daya daga cikin mambobin Hukumar Hajji ta ƙasa (NAHCON), Sheikh Muhammed Bin-Usman, ya bayyana cewa cin hanci da rashawa sun yi ƙamari sosai a harkokin aikin Hajjin Nijeriya, musamman a aikin Hajjin da aka kammala na shekarar 2025.

Bin-Usman, wanda shi ne kwamishinan da ke kula da yankin Arewa maso Yamma a hukumar, ya yi wannan zargi ne a shirin “Rigar Kaya” na Lumana Radio International da ke Kano a ranar Lahadi.

Ya ce, NAHCON ta bai wa wasu kamfanonin Saudiyya kwangilar gudanar hidima na aikin Hajji na 2025 cikin sirri, har ma da daraktan da ke kula da ayyukan hukumar bai san da kwangilar ba.

Ya ƙara da cewa, Dokar NAHCON ta 2006 ta tanadi cewa kwamishinoni guda shida da ke wakiltar yankuna shida na ƙasar su kasance cikin yanke shawara, amma hakan ba a cika aiwatar da shi ba.

Ya kawo misali da shekarar da ta gabata lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya tallafa da naira biliyan 90 domin rage kuɗin aikin Hajji, amma kwamishinoni shida da wasu manyan jami’an NAHCON ba a sanar da su yadda kuɗin suka tafi ba.

“A aikin Hajjin da aka kammala na 2025, NAHCON ta bai wa wani kamfanin Saudiyya kwangila ba tare da sanin kwamishinoni shida da ke wakiltar yankuna shida na ƙasar ba.

“Daraktan da ke kula da ayyuka a hukumar ba ya da masaniya kan wannan kwangila da aka bai wa kamfanin Saudiyya. Ya nuna rashin amincewa, har ma ya ce zai kai rahoto ga shugaban ƙasa. Wannan abin kunya ne sosai.

“Wuraren da cin hanci da rashawa ke yawan faruwa kuma ake rufe gaskiya su ne: bayar da kwangila ta masaukin mahajjata, abinci, da sufuri, inda ake haɗa baki da wasu daga wajen hukumar.”

Bin-Usman ya ƙara da cewa, ɗaya daga cikin daliban sa daga Madinah, wanda ya san yadda ake tafka badakala wajen neman masauki da sufuri da abinci, ya gargade shi da irin waɗannan mummunan ayyuka.

“Ba zan bari wani ya aikata laifi ni kuma a ce ni ne zan ɗauki laifinsa ba, domin ni ina da suna da mutunci da zan kare. Abin takaici, yanzu ana ambaton NAHCON saboda mummunan suna, mu kuma muna ciki amma ba za mu iya yin shiru ba. Dole ne mu faɗi gaskiya ga duniya abin da ke faruwa,” inji shi.

”A matsayi na na Kwamishina a NAHCON, idan taro ya taso, da kudi na na ke zuwa, in biya duka kwanakin da zan yi da kudi na, sai daga baya wani lokacin ma har na cire rai, in yi ta bi kafinnan.

Bin-Usman ya bukaci Hukumar EFCC ta gudanar da bincike a kan ayyukan NAHCON.

Ana rahoton cewa EFCC tana gudanar da bincike kan zargin karkatar da sama da naira biliyan 50 a ayyukan Hajjin 2025, kuma tana tambayoyi da hukuma Shugaban NAHCON, Abdullahi Pakistan.

Ana zargin Pakistan da kashe naira biliyan 25 wajen haya da tsare-tsaren tantunan mahajjata a Saudiyya, biliyan 7.9 wajen masaukin gaggawa, da biliyan 1.6 wajen kuɗin tafiyar matan jami’an gwamnati.

Hukumar EFCC ta tsare Kwamishinan NAHCON mai kula da Tsare-tsare, Ma’aikata da Kuɗi, Aliu Abdulrazak, tare da Daraktan Kuɗi da Lissafi, Aminu Muhammed, a watan Satumba dangane da wannan badakala.

A baya, yayin zaman sauraron jama’a a Majalisar Wakilai, Shugaban NAHCON ya amince cewa akwai “Abubuwan da basu dace ba da ake tafkawa a hukumar” a cikin hukumar, inda ya yi alƙawarin goyon bayan duk wani ƙoƙari na tabbatar da gaskiya da rikon amana.

By ukarofi