Shahararrun Mutanen Afrika: An Karrama Dr. Dauda Lawal A Birnin Landan

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Cibiyar Karrama Shahararrun Mutane na Afrika da ke Landan ‘African Achievers Award’ ta karrama Dr. Dauda Lawal Dare a shekaran jiya Juma’a, 10 ga watan Disamba a Fadar Kensisngton dake Birnin Landan.

Kambun karramawa na ‘African Achievers Award’ shi ne mafi girma da tasiri a duniya wanda ya ke zaƙulowa tare da karrama mutane masu muhimmanci da suke taka rawa wurin bunƙasar nahiyar Afirka.

Taken taron bana shi ne: ‘Samar da hanya ga mazauna ƙasashen ƙetare su zuba jari don bunƙasar tattalin arzikin Afirka’.

Mujallar Forbes ta ruwaito cewa, wannan bikin karramawa na ‘African Achievers Awards’ na daga cikin mashahurai kuma mafi tasiri a bukukuwan da ake gudanarwa a Jami’ar Cambridge.

Dr. Dauda Lawal wanda tsohon Babban Daraktan Bankin First Bank ne, shi ne kuma shugaban Kamfanin Credent Capital and Advisory LTD dake Abuja, ya shiga jerin shugabanni daga Afrika da wannan cibiya ta karrama. An karrama shi ne saboda irin gudummawarsa ga fannin tattalin arziki da kuma samar da hanyoyin ayyukan yi ga musamman matasa.

Kafin bikin karramawar an gudanar da lakca a ranar Alhamis 9 ga watan Disamba a Jami’ar Cambridge, bisa jagorancin Lord Simon Woolley.

Daga cikin shugabannin da aka zaɓa don gabatar da jawabi akwai Dr. Dauda Lawal, wanda ya yi fashin baƙi kan maudu’i mai taken : “tattaro hanyoyin zuba jari daga mazauna kasashen ƙetare, don bunƙasar Afrika”.

A jawabin nasa, Dauda ya bayyana cewa, wannan maudu’in ya zo a daidai kan gaɓa, domin ana buƙatar gabato da hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin Afrika.

Ya kawo matsalolin da mazauna ƙetare ke fuskanta wurin taimakawa yankin Afrika, tare da bijiro da mafita domin samar da hanyar zuba jari ga tattalin arzikin yankin.