Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe
A wani biki mai cike da tarihi da nishaɗi, ƙungiyar sha’irai ta Jihar Gombe ta gudanar da gagarumin taro inda ta karrama shugaban ƙaramar hukumar Gombe, Barista Sani Ahmadu Haruna, bisa namijin ƙoƙarinsa wajen tallafawa addini da kuma bunƙasa harkar sha’irai a faɗin jihar.
An gudanar da wannan biki a babban zauren ƙungiyar, inda manyan malamai, shugabannin addini, fitattun mawaƙa da ɗaruruwan mambobin ƙungiyar suka taru domin nuna farin ciki da girmamawa ga jagoran wanda ya zama ginshiƙin ci gaban al’umma.
Shugaban ƙungiyar sha’irai, Malam Salisu Awadatu, yayin gabatar da lambar yabo ya bayyana cewa wannan karramawar ta kasance sakamakon kishin addini da kyakkyawan shugabanci da Barista Sani ke nunawa, musamman yadda yake mara baya ga kowace hidima da ta shafi ƙungiyar da kuma shirye-shiryen da ke girmama fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam).
A nasa jawabin shugaban Ƙaramar hukumar Gombe, Barista Sani Ahmadu Harruna ya bayyana farin cikinsa da godiya ga ƙungiyar bisa wannan karamci, yana mai tabbatar da cewa zai ci gaba da tallafawa ayyukan da ke ƙara ɗaukaka addini da raya al’adun sha’irai.
Ya kuma yi kira ga matasa da mazauna ƙaramar hukumar da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai, da kishin ci gaban gari da jihar gaba ɗaya.
Bikin ya ƙare cikin nishadi, inda fitattun sha’irai suka rera waƙoƙin yabo da addu’o’in fatan alheri, tare da bayyana shugaban a matsayin gwarzon da ya cancanci irin wannan lambar yabo.
