Matatar Fatakwal ba ta sayerwa ba ce, inji NNPC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya yi watsi da jita-jitar shirin sayer da Matatar Fatakwal dake jihar Ribas daga gwamnati, yana mai jaddada ƙoƙarinsa na kammala aikin gyara ta yadda za ta koma cigaba da aiki yadda ya dace.

Shugaban Kamfanin, Bashir Ojulari ya sanar da haka a wani ɗakin taron manyan jami’ai a hedikwatar kamfanin dake Abuja.

Ya ce, matakin ya biyo bayan nazari game da kayayyakin aiki da kuɗaɗen gudanarwa na matatun Fatakwal, Kaduna da Warri, yana mai cewa sai an kammala gyare-gyarensu ne za a koma aiki da su.

Ojulari ya bayyana cewa, an samu ci-gaba wajen ayyuka akan baki ɗaya matatun inda ake buƙatar kayayyakin aiki na zamani domin kammala ayyukan da ake yi akansu.

Shugaban na NNPCL ya jaddada haka ne a yayin da ake yaɗa jita-jitar sanya matatar a kasuwa a lokacin da ya halarci wani taron ƙara wa juna sani na OPEC a Vienna dake ƙasar Austriya, inda ya furta cewar akwai zaɓi da dama akan matatun, lamarin da ya haifar da jita-jitar sayerwan.

By Babaji