Daga UMAR GARBA a Katsina
Ƙungiyar sanatocin Arewacin Najeriya ta yi Alla-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu fararen hula 35 a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a Jihar Zamfara.
Cikin wani saƙon jaje da ƙungiyar ta aike ranar Laraba a Abuja, shugaban ƙungiyar Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua, sanatan Katsina ta tsakiya, ya jajanta wa al’ummar yankin musamman iyalan waɗanda lamarin ya shafa.
A farkon makon nan ne ‘yan bindiga suka yi wa wasu mutanen yankin yankan rago duk kuwa da biyan kuɗin fansa da aka ce iyalansu sun yi domin kuɓutar da su.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga masu sace mutane domin neman kuɗin fansa.
