Bauchi/Gombe: NNPC ya haƙa rijiyoyin mai huɗu a Kolmani

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Darakta a Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) mai suna Yusuf Usman, ya ce kamfanin ya yi nasarar haƙa rojiyoyin mai guda huɗu a yankin Kolmani da ke Jihar Bauchi.

Ya jaddada ƙoƙarin Kamfanin na faɗaɗa ayyukan haƙo albarkatun mai da gas a shiyyar arewacin Nijeriya.

Daraktan ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Kaduna, yayin taron bitar ayyukan gwamnati ga al’umma da Gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya a Arewa House.

Ya kuma ce, a ƙarƙashin shirye-shiryen Shugaba Bola Tinubu na samar da makamashi na CNG da LNG, ana aikin gina tashoshinsu guda biyar a jihar Kogi.

Kazalika, ya ce tashoshin za su taimaka wajen faɗaɗa hanyoyin samarwa da raba gas cikin sauƙi a yankin arewacin Nijeriya.

By Babaji