
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Talata wasu ƴan bindiga suka farmaki jami’an haɗaka na sojoji da ƴan bijilante a yankin Dogon Ruwa dake Gundumar Bashar na Ƙaramar Hukumar Wase a Jihar Filato.
Lamarin da ya yi sanadin rasa rayukan sojoji biyu da ƴan bijilante biyu.
Shaidu sun ce, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na dare a lokacin da jami’an suke sintiri a yankin sakamakon samun rahoton yunƙurin kai hari daga ƴan ta’adda.
Maharan sun halaka jami’an ne a lokacin da suka yi shigar ba-zata da yi musu ruwan alburusai.
Sarkin Dogon Ruwa, Abdullahi Yakubi ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce an cimma jami’an ne ba tare da sun ankara ba.
Ya kuma ce, maharan sun tsere da bindigu da kayan jami’an sojojin da suka kashe.
Wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim Sale ya ce al’amarin ya jefa yankin da al’umma cikin halin ɗar-ɗar.
Saidai, ba a samun ji ta bakin kakakin jami’an atisayen ‘Safe Haven’, Manjo Samson Nantip Zhakom ba zuwa lokacin haɗa rahoton.
