
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba Gwamnan Jihar Benuwai, Hyacinth Alia, ya sanar da rushe baki ɗaya tawagar jagororin ma’aikatun jihar (SEC) a wani yunƙuri na yi wa gwamnatinsa garambawul.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin zaman SEC karo na 12 a Gidan Gwamnatin jihar dake Makurɗi, lamarin da ya sa ake ganin hakan a matsayin salo na yi wa tawagar manyan jami’an gwamnatin nasa tankaɗe yayin shiga zangon mulkinsa na gaba.
Sakataren yaɗa labaransa, Tersoo Kula a wata sanarwa, ya ce baya ga haka gwamnan ya sanar da naɗin Barista Moses Atagher a matsayin sabon shugaban ma’aikata.
Moses Atagher, wanda ɗaya ne daga cikin masu faɗa a ji a jihar, ya yi aiki sau biyu a matsayin antoni janar kuma kwamishinan shari’a a Benuwai.
Ya kuma yi aiki a matsayin darakta manaja na riƙo a Bankin Jingina na Tarayya, wato Federal Mortgage Bank, lamarin da ke nuna ƙwarewarsa a fannin gudanarwa.
Gwamna Alia ya kuma yi godiya ga kwamishinonin masu barin gado bisa ƙoƙarinsu na hidimta wa jihar da al’ummarta a tsawon shekaru biyu da suka gabata.
