Bauchi: Shugaban hukumar zaɓe, Ahmed Makama ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Hukumar Zaɓe ta jihar Bauchi (BASIEC), Alhaji Ahmed Makama ya rasu a Abuja bayan wata jinyar rashin ta ƙaramar lokaci da ya yi fama da ita.

Marigayin, wanda tsohon kwamishinan zaɓe na reshe ne a Jihohin Taraba da Nasarawa, ya rasu ne a ranar Talata, 29 ga watan Yuli, 2025.

A wani saƙon ta’aziyya da aka fitar a ranar Laraba kamar yadda WikkiTimes ta ruwaito, Gwamnan jihar, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar mamacin a matsayin babban rashi ga jihar da ma ƙasa baƙi ɗaya, yana mai la’akari da gudunmuwarsa ga ci-gaban dimukraɗiyya a Nijeriya.

Ya jinjina wa ƙoƙarinsa wajen tabbatar da gaskiya da adalci yayin gudanar da zaɓuka a matsayin na shugaban BASIEC.

Gwamna Bala, ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da ƴan uwa da abokan arziƙi, da BASIEC da kuma Masarautar Misau bisa rashin, yana mai addu’ar Allah ya gafarta masa, Ya kuma sa ya huta.

Gabanin rasuwarsa, aikin marigayin na kwanan nan shi ne sanya ido a zaɓen cike gurbi na Ƙaramar Hukumar Shira da aka gudanar a ranar 24 ga watan Mayu, 2025.

By Babaji