Shanghai: An yi wa sama da mutane miliyan 24 gwajin cutar COVID-19 a rana guda

Daga CMG HAUSA

A jiya Litinin, mahukuntan birnin Shanghai suka bayyana cewa, an kammala karɓar samfurin gwajin cutar COVID-19 daga al’ummar birnin su sama da miliyan 24, a wani mataki na daƙile bazuwar annobar, wadda ta sake ɓulla a sassan birnin.

Wata sanarwa da aka fitar ta nuna cewa, an sanya birnin Shanghai cikin matakin kulle na wucin gadi, bayan da adadin masu harbuwa da cutar ta COVID-19 ya ƙaru matuƙa a ‘yan kwanakin baya bayan nan.

Kaza lika, sanarwar ta ce a yanzu haka mahukuntan birnin na ci gaba da ayyukan gwaji, da killace masu ɗauke da cutar, tare da bincike da tantance yanayin bazuwar ta. Za kuma a ci gaba da aiwatar da waɗannan matakai bisa tsari.

Jami’an lafiya sama da 38,000 daga larduna da yankunan ƙasar Sin 15 ne suka isa Shanghai, domin aikin dakile cutar ta COVID-19, a cewar hukumar kiwon lafiyar ƙasar Sin NHC.

Da safiyar Talatar nan, mahukuntan birnin sun ce a jiya Litinin, an tabbatar da harbuwar mutane 268 da cutar, an kuma gano mutane 13,086 ɗauke da ita ba tare da sun nuna alama ba.

Fassarawa: Saminu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *