Shawarar Bankin Duniya kan shigo da mai na iya jefa Nijeriya cikin matsala — Masana

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wasu ƙwararrun masana a fannin man fetur sun bayyana damuwarsu kan sabuwar shawarar Bankin Duniya ga Nijeriya, inda suka gargaɗi cewa hakan na iya maida ƙasar baya zuwa dogaro da shigo da man fetur daga waje, abin da suka ce ya saɓa wa burin ci gaban tattalin arziki da kuma dokokin ƙasar.

A cewarsu, shawarar da bankin ya bayar cikin rahotonsa na sabunta tattalin arzikin Nijeriya, wadda ke ƙarfafa ƙara shigo da mai da kuma cikakken ’yantar da kasuwar man fetur ta ƙasa (downstream), ba ta zo a lokacin da ya dace ba, kuma na iya kawo koma baya ga ƙoƙarin ƙasar na dogaro da kanta a fannin makamashi.

Wani masanin tattalin arzikin makamashi, Farfesa Ken Ife, ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a talabijin, inda ya ce duk da cewa wasu ɓangarori na rahoton Bankin Duniya suna da inganci, amma shawarar da ta shafi shigo da mai na barazana ga burin Nijeriya na ƙarfafa tace mai a cikin gida.

Ya ce, ba daidai ba ne a ce wa ƙasa da ke ƙoƙarin kafa tsarin dogaro da kanta ta tattalin arziki ta koma kan tsohuwar hanyar shigo da mai daga ƙasashen waje. A cewarsa, irin wannan shawara na raunana duk wani ƙoƙari da Nijeriya ke yi na bunƙasa masana’antun cikin gida da rage dogaro da waje.

Farfesa Ife ya kuma jaddada cewa wannan shawara ta saba kai tsaye da tanadin dokar masana’antar mai ta ƙasa, wato Petroleum Industry Act, wadda ta tanadi cewa dole ne a bai wa matatun cikin gida fifiko wajen samar da ɗanyen mai ta hanyar tsarin “Domestic Crude Obligation”.

A cewarsa, dokar ta fito ƙarara cewa fifiko ya kamata ya kasance ga tace mai a cikin gida, don haka shawartar Nijeriya ta bar wannan hanya ba kawai sabawa manufofin gwamnati ba ne, har ma take karya doka.

Haka kuma, ya yi gargaɗin cewa ƙara shigo da mai daga ƙasashen waje zai ƙara jefa Nijeriya cikin haɗarin rikicewar kasuwar duniya, tare da hanzarta ƙarewar kuɗaɗen musayar waje (foreign eɗchange), sannan kuma ya rage sha’awar masu zuba jari a fannin tace mai a cikin gida — musamman a wannan lokaci da kamfanoni masu zaman kansu ke ƙara saka hannun jari a ɓangaren.

Ya ƙara da cewa, Nijeriya na kan hanyar ƙara ƙarfin tace mai har ta wuce buƙatar cikin gida, abin da zai iya ba ta damar zama mai fitar da makamashi zuwa ƙasashen waje, don haka ba da shawarar komawa ga shigo da mai na nuna rashin la’akari da wannan ci gaba.

Shi ma wani masanin makamashi, Kelɓin Emmanuel, ya goyi bayan wannan ra’ayi, inda ya soki matsayin Bankin Duniya, yana mai cewa shawarar ta yi nesa da gaskiyar halin da kasuwar makamashi ke ciki a halin yanzu.

A cewarsa, an ma rahoto cewa Bankin Duniya ya cire rahoton da ya janyo ce-ce-ku-ce daga shafinsa na yanar gizo, abin da ke nuna cewa akwai matsala a cikin shawarar da aka bayar.

Masana na ganin cewa a maimakon komawa ga tsohon tsarin shigo da mai, ya kamata Nijeriya ta ƙarfafa matatun cikin gida, ta bunƙasa masana’antu, tare da tabbatar da cikakken aiwatar da dokokin da aka kafa domin inganta tattalin arzikin ƙasa.

By ukarofi