Shehu Mahi zai halarci mauludin Inyass a Kano – Sheikh  Tijjani Auwalu

Spread the love

Daga MUHAMMADU MAJITTABA a Kano

Shugaban ƙungiyar Majama’u-Ahbab na ƙasa, wato ƙungiyar da ta ke shirya gagarumin Maulidin Shehu Ibrahim Inyass RT kamanin shekaru 40 da suka wuce, Sheikh Tijjani Sani Auwalu, ya tabbatar da cewa sun yi magana baka da baka da Khaliphan Tijjaniyya Faira Sheikh Ahamad Mahi cewa da ikon Allah in ya nufa da ransa da lafiyarsa ya tabbatar wa da Muridan Shehu, masoya Manzon Allah da masoyan Shehu Ibrahim Inyass, wanda ake Maulidinsa duk shekara, saboda san son da manzon Allah, da ahalinsa da sahabbansa cewa mutanen Nijeriya, Afirka da ma ɗaukacin al’ummar da za ta zo, Maulidin Shehu, na wannan shekara na ƙasa, to a Maulidin da aka shirya a Kano zai bayyana za a ganshi, za a yi tozali da shi, da ikon Allah, kamar dai yadda Shugaban Majama’u’Ahbab na ƙasa Sheikh Tijjani Sani Auwalu ya bayyana a wata ganawarsa da manema labarai a yammacin Talatar da ta gabata.

Haka kuma ya ce Khalipha Shehu Ahmad Mahi, Shehu Ibrahim Inyass ya ce yana nan a kan tafarkin ‘yan uwansa da suka gabata kamar su Shehu Abdullahi, Shehu Dam., Shehu Tijjani Inyass, wanda da kan su su ke zuwa wannan Mauludi na shekaru 40 da suka gabata tun ana yi a falo har aka zo ana yi a fili gashi kuma yau duk inda ake wannan Mauludi na Shehu Ibrahim Inyass za ka ga gari cika yake da albarka ta inda mutane su ke zuwa daga sassa daban daban na jihohi da ƙasashe duniya, domin dai a haɗu ayi zumunci a ayi farin ciki a isar da saƙon jaddada saƙon Manzon Allah, da masoyansa, wanda kuma ƙaunarsa da ma’akin Allah ta jawo masa wannan karama da ake gagarumin taro domin Maulidin Iyanss.        

Shugaban Majamau Ahababu na ƙasa ya ƙara da cewa kafin ranar Maulidin an yi mako guda domin bayyani akan Shehu Ibrahim Inyanss, akan gudummawarsa ga addini iliminsa tarihinsa baiwarsa da sauransu, wanda fitattun malamai daga Nijeriya da wajenta za su gabatar a tsawon mako guda kafin gagarumin taron da shugaban ƙasa ko wakilinsa da kuma mai masauƙin baki gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, da maƙarraban gwamnatin Kano da kuma shehunan malaman Tijjaniyya irinsu, Sheikh Shehu Mai Hula, Sheikh Usman Zangon Barebari shugaban Majama’u’ahbabu na ƙasa da sauransu, za su kasance a wajen taron da kuma gabatar da jawabi daga wasu manyan baƙin a wannan Maulidi Shehu.

A ƙarshe ya yi kira ga ɗaukacin Musulmi musamman mabiya ɗariƙar Tijjaniyya masu wannan mauludi da sauran al’umma da cewa su haɗa kan su, domin rabuwa rauni ne, haɗin kai shi ne ƙarfi masu san Maulidin shehu Inyass, ya kamata ayi rana ɗaya, a waje ɗaya, idan kana da muradin yin maulidin Shehu, to zai yi kyau kayi kafun wannan rana ko bayan wannan rana ko ka gayyace mu ko baka gayyace mu ba zamuje, har masoyin manzon Allah Shehu da sauransu ta kowa da kowa ne wannan taro ikon Allah ne babu wanda ya ke da tasiri akan yin sa sai Ubangiji babu wanda zai iya cewa shi ya ke tara wannan jama’a, babu wanda kuma zai iya hanawa don haka kowa ya fahimci wannan abu, ba jayayya ba ne, ba faɗa ba ne, balle mu ce a mai da wuƙar, don haka ya yi kira ga masu zuwa wannan maulidi na shehu a makon ƙarshe na watan Rajab, da su kiyaye dokokin tuƙi musamman direbobi da ƙa’idojin hanya a cigaba da addu’ar zaman lafiya Nijeriya da yin wannan taro lafiya kamar yadda aka saba a kowane lokaci.

By ukarofi