Ɗalibar Jami’ar Bayero ta binciko yadda ake gane cutar Kansa a hoton hannun mace – Farfesa Darma

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Shugaban tsangayar Nazarin Kimiyyar Halittun Fili da na Voye da Harhaɗa Magunguna na Jami’ar Bayero, Farfesa Tijjani Hassan Darma, ya bayyana cewa yanzu haka jami’ar ta gano yadda ta hanyar ɗaukar hoton mace za a iya gano tana da Kansa ko babu, ba tare da wani vata lokaci ba ko wani dogon gwaje-gwaje, a karon farko a tsakanin jami’o’in duniya, musamman da aka lura mata sun fi maza kamuwa da cutar Kansa, kamar yadda jami’ar ta gano ta hanyar saka gasa a tsakanin ɗaliban kimiyya, inda wata ɗalibar Jami’ar Bayero a cibiyar ASPAK da ke ƙarƙashihn Farfesa Halima Galadanchi ta gano wannan fasaha bayan gasar da aka saka musu kuma ta samu wannan kyaututtuka a nasarar da ta yi, inji Farfesa Tijjani Hassan Darma a lokacin babban taron ƙasa da tsangayar da ta haɗa kwalejoji uku ta shirya a karo na bakwai.

Ita ma cibiyar binciken aikin noma CDA ta binciko irin dawa daidai da yanayin ƙasashe masu samun ƙarancin ruwan sama ko fari da dawar da ke da garin ta ke daɗewa baya lalacewa, sai kuma gano macen dabino tun ta na jaririya wanda zai ba da dama a shuka dabino mace da yawa namiji kaɗan don amfanin al’umma.

Har ila yau, Farfesa Darma ya ce sassa uku da suka haɗa da sashin nazarin kimiyyar rayuwar halittu da sashin kimiyyar lissafi da abubuwan da ido ke iya gani har ma da wanda baya gani da kuma sashin da kuma sashin harhaɗa magunguna domin bajekolin ilimi don yin nazarin bincike da zai amfanar da masana da jami’o’i da kuma sauran al’umma.

Tijjani Hassan Darma ya ƙara da cewa binkicen wata hanya ce da ake yin amfani da ilimin masana domin magance wata matsala da kuma wani abu da ake ganin zai iya faruwa, ya ce maƙasudun taron, shi ne domin haɗa masana da bajekolin fasahar su da kuma taimakawa juna wajen a gudu tare a tsira tare, dangane da ya na yin ƙarin kuɗi da aka samu a jami’o’in ƙasar nan kuma ya ce jami’ar Bayero ƙarƙashin shugabanci Mataimakin Jami’ar Farfesa Sagir Abbas, ya taka rawa sosai wajen nemo tallafi daga shugabanni, ‘yan siyasa, kamfanoni, da ɗaiɗaikun jama’a domin tallafawa ɗaliban da basu da ƙarfi wajen samun kammala karatunsu a wannan tsangaya, inda kashi 90 cikin 100 sun samu kammala karatunsu ta hanyar wannan tallafi na jami’ar da kuma shugabanta. 

Farfesa Darma ya bayyana takaicinsa na rashin kayan aiki na zamani da kula da masu basira irin waɗannan daga hukumomin ƙasa wanda yanzu haka wannan yarinya ƙasashen Turai sun ɗauke ta.

By ukarofi