Sheikh Idris Dutsen Tanshi da jami’an tsaro su ka cafke a Bauchi ya samu belin kotu

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Babbar Kotun Majistare ta ɗaya a Jihar Bauchi wacce Mai Shari’a Abdul Fatah Ba Shakoni ke jagoranci a ranar Talata da ta gabata ne ta bayar da belin wani firaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Idris Abdul’aziz akan kuɗi Naira miliyan ɗaya da madadin su na fitattun mutane uku.

Kotun ta zayyana mutanen da za su karɓi belin shehin malamin da suka haɗa da Hakimi da shehin ke mazauni a ƙarƙashin mulkinsa, babban sakatare dake cikin mulkin gwamnatin jihar Bauchi wanda zai nuna takardar mallakar kadara da kuɗin ta ba zai gaza Naira miliyan biyar ba, haɗi da wani shahararren malami ma’abucinsa.

Sheikh Idris Abdul’aziz dai a ranar Litinin da ta gabata ne jami’an tsaro na ‘yan sanda suka cafke shi bisa zargin yin kalaman ɓatanci da ya jaddada husuma a tsakanin shahararrun malamai tare da rarraba kawunansu da na ɗaukacin al’ummar jihar Bauchi, da yake da nasabar tada zaune tsaye, suka kuma gurfanar da shi a gaban kotun babbar majistare ta ɗaya dake garin Bauchi.

Tun da farko dai hukumar rundunar tsaro ta ‘yan sandar jihar Bauchi ne suka gayyace shi zuwa shalkwatar rundunar da zummar fayyace masu wasu kalamai da ake zargin sun fito daga bakinsa, cikin tafsiransa na watan Azumi da ya gabata, da ake zargin kalaman suna da nasaba da ɓatanci wa Shugaban Halitta, kuma ma’aiki na addinin Islama.

Zargin kalaman haddasa husuman dai ya yi kiciɓis da soke-soken wasu fitattun malamai na jihar Bauchi, yayin da wasu kuma suka goyi bayan furucin kalaman, da cewar suna da sahihanci, lamarin da ya haddasa rabuwar kawunan ɗaukacin malaman na jihar Bauchi.

Alƙalin kotun ya ce, “bisa alamun sahihancin maganganu da suka gabata, kuma muhimmi bisa son kamanta adalci, wannan kotu ta ga ya dace ta bayar da belin Shehin malamin da aka nema tun farko daga gare ta bisa cika tsauraran sharuɗɗa da ya kamata a yi haƙuri da su, la’akari da nauyin laifuka da ake zargin shehin da aikatawa, haɗi da dubi da yanayi da ake ciki.”

Majistare Abdulfatah Shakoni ya ƙara da cewar, “Babu wata dama wa wannan kotu, a wannan gava ta bayyana wani son zuciya, domin batu ne na doka ko shari’a, na haƙiƙa da halin da ake ciki wanda kotu ta duba a matsayin tausayawa ko mai taɓa zuciya.”

Lauyan ma’aikatar Shari’a ta jiha, Barista Aliyu Ibn Idris ya gabatar wa kotun buƙatar ofishin Kwamishinan Shari’a ya karɓi ƙarar daga hukumar ‘yan sanda domin cigaba da gabatar da ita wa kotu, wacce ta lamunce da hakan, tare da ɗage zaman ta zuwa 24 ga wannan wata na Mayu, 2023 domin sauraron ƙarar.

Ɗaya daga cikin lauyoyi masu kare wanda ake tuhuma, Barista Abubakar Sadiq Ilelah da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ɗage zaman kotun, ya bayyana farin cikinsa da samun beli wa shehin, tare da bayar da tabbacin za su cika ƙa’idojin belin kafin ranar Talata ta shuɗe.

Dangane kuwa da buƙatar na ofishin kwamishinan shari’a na amshe ƙarar daga hukumar ‘yan sanda kuwa, lauyan ya ce ofishin Kwamishinan Shari’a walau a gwamnatin tarayya yana da hurumin amshe ƙara dake gaban kotu bisa sahalewar tanade-tanade dake sashi na 211 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, wanda aka yi wa gyara.

Shi ma da yake zantawa da manema labarai a farfajiyar kotun, babban sakatare a ma’aikatar Shari’a ta jihar Bauchi, Barista Aliyu Ibn Idris ya ce yin nazari akan abubuwa da farkon shigar da ƙarar ya ƙunsa zai bai wa ofishin su damar walau sauya tuhumce-tuhumcen ƙarar ko kuma akasin haka.

Barista Aliyu Idris ya ce, “Idan sun gamsu da tsarin tuhumce-tuhumce da jami’an ‘yan sanda suka tanada a cikin farkon ƙarar, shi ke nan ba wani ka-ce-na-ce, sai su cigaba da gabatar da ƙarar a gaban kotu, idan kuma an samu akasi, ya zama wajibi su sake tsara tuhumce-tuhumcen, haɗi da gabatar da shaidun da suka wajaba.

Idan za a iya tunawa dai, wasu ƙungiyoyin addinin Musulumci ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar ‘Fitiyanul Islam’ a kwanakin baya sun zargi Shehi Idris Abdul’aziz da yin kalaman vatanci wa waɗansu jigajigan malamai mazauna Bauchi, har ma da Ma’aikin Allah, lamarin da suka yi wa kallo tamkar maganar savo.