Daga MOHAMMED ALI a Gombe
Ƙungiyoyin hadin Kan Leburorin Motocin Tifa na Awala sama da mutum dubu goma da ke Jihar Gombe suna roƙon Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da ya kawo musu tallafin gaggawa don ciyar da dubban dattawan ƙungiyar da ƙarfinsu ya ƙare.
Har ila yau, suna kuma tunatar da Gwamna akan alƙawuran da ya yi na tafiya tare da su wajen ƙara musu ƙarfin gwiwa kamar sauran ƙungiyoyin jihar.
Waxannan koke-koke sun fito ne daga bakin sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar Alhaji Abubakar Bose lokacin da yake hira da ’yan jaridu, jim kaxan bayan an rantsar da shi a matsatsen harabar harkokinsu.
Abubakar Bose ya yi nuni da cewa, jihar Gombe babu ƙungiyar da ta baiwa Gwamna Yahaya ƙuri’u a lokutan zaɓensa na zangoɗaya dana biyu kamar ƙungiyar leburorin Tifa, don haka yana kira gareshi ya dubesu a wannan karon ya taimakesu da katafaren filin gudanar da ayyukansu ya kuma baiwa ’yan ƙungiyar wani matsayi a gwamnatin sa, ko na mai bashi shawara (S.A) ko na mataimaki a fannin leburanci.
“Domin a yau, ƙungiyar mu ta taimaka ba kaxan ba wajen Gina Jihar Gombe ta fannonin ci gaba iri-iri cikin shekaru 50 da aka kafa ta saboda haka mun cancanci tallafin gwamnatinshi, ko da yake ya nuna mana kauna amma dai da ya shigar damu cikin gwamnatinsa.
Sabon shugaban sai ya jawo hankalin duk ’yan ƙungiyar, da su ci gaba da baiwa Gwamnati goyon baya, su kuma zama masu bin doka da oda domin a kashedin shi “wannan karon ƙungiya ba-zata lamunci sace-sace da rashinɗa’a ba”.
A takaitaccen bayanin shi lokacin da yake mika ragamar mulki tsohon shugaban Kungiyar Alhaji Ahmadu Yana kira yayi ga dukkan mambobin ƙungiyar da su tabbata sun baiwa sabon shugaban Abubakar Bose duk irin goyon bayan da yake buƙata, kuma kuma su yi aiki akan tafarkin gaskiya da riƙon amana kamar yadda aka dora ƙungiyar a kai tun sama da shekaru 50 da suka wuce.
A nashi sakon fatan alheri ga sabbin Shugabannin, tsohon sakataren ƙungiyar, Alhaji salisu Adamu ya yi godiya ga Allah da aka kamala bikin rantsuwar lami lafiya kuma yana fata zaɓaɓɓun shugabannin za su ƙara ciyar da ƙungiyar gaba fiye da take a yanzu.
Sabbin shugabannin ƙungiyar sun haxa da Abubakar Bose (Shugaban-ciyaman), sai Muhammad Usman (Mataimaki-Deputy), sai Zubairu Saleh (Sakatare). Akwai kuma Jami’in kuxi Umar Abdullahi sai Ma’aji Sale Dogo, sai kuma Ali Bogo a matsayin kakakin ƙungiyar (PRO).
