Daga JOHN D. WADA a Keffi
Shugabar Babbar Jami’ar Jihar Nasarawa dake birnin Keffi, hedikwatar ƙaramar Hukumar Keffi a jihar, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta ce zuwa yanzu cikin shekaru 25 da suka gabata jami’ar ta samu ɗimbin nasarori a duka matakai.
Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta bayyana haka ne a lokacin da take tattaunawa da manema labarai a ofishin ta game da wani babban taro na musamman na yaye ɗalibai da ake kira conɓocation ceremony a turance tareda bikin murnar cikar jami’ar shekaru 25 da kafuwa wanda aka gudanar a jami’ar kwanan nan.
Ta bayyana cewa kawo yanzu jami’ar ta kuma yaye dalibai da dama da a yanzu haka suka kware a wuraran ayukansu daban-daban inda suke cigaba da ba da gagaruman gudumawa a inda suken don cigaba ƙasar nan da duniya bakiɗaya.
Farfesa Sa’adatu ta kuma yaba wa hangen nesa da wanda ya kafa jami’ar wato Dokta Abdullah Adamu ya yi na kafata inda ta ce tabbas tarihin jami’ar ba zai kammala ba ba tare da an ambato sunarsa ba.
Shugabar babbar jami’ar jihar ta Nasarawa farfesa Sa’adatu Hassan Liman har ila yau ta kuma yaba wa kokarin duka tsofaffin shugabannin jami’ar inda tace tabbas suma sun taka mahimmin rawa wajen cigaba da ake samu a jami’ar a yanzu.
Ta kuma yi amfani da damar inda ta sanar cewa a yanzu al’ummar jihar bakidaya musamman iyaye na cigaba da alfa’arin kasancewar jami’ar a matsayin wadda ake ji dashi a ƙasar nan da nahiyar Afirka dama duniya bakidaya inda ta kara da cewa a yanzu haka hukumomi da cibiyoyi dabandaban na cigaba da sha’awar alaka da jami’ar a duka matakai.
Ta yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule wanda shine babban baƙon jami’ar shima inda tace gwamnan yana matukar tallafa wa jami’ar a duka fannoni Idan akayi la’akari da dinbin ayyukan cigaba da suka hada da tsabbin hanyoyi da gine-gine da gyare-gyare da gwamnatinsa ke cigaba da gudanar a jami’ar zuwa yanzu.
Daga nan sai ta kuma yin amfani da damar har ila yau inda tayi kira na musamman ga duka tsofi da daliban jami’ar na yanzu gabadaya su cigaba da kasancewa jakadun jami’ar na kwarai kamar yadda akasan su don cigaba da kare sunar jami’ar a idon duniya bakidaya.
Wakilinmu a jihar ya kuma rubuto cewa a taƙaice kimanin ɗalibai sama da dubu 25 ne a matakin digiri na farko da kuma matakin digiri na biyu aka gabatar musu da satificate a hukumance tareda bikin cika shekaru 25 da kafuwar jami’ar ta Nsuk din da sauran su ayayin babban taron mai dinbin tarihi kamar yadda shugaba Farfesa Sa’adstu Hassan Liman ta sanar a yayin tattaunawar.
