Shettima zai jagoranci tawagar aikin hajji daga Nijeriya

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, zai jagoranci tawagar mahajjata daga Najeriya zuwa Saudiyya domin aikin Hajjin bana na 2025. Shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh, ne ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a talabijin. Ya ce Shettima zai gudanar da ibadar ne a matsayinsa na Musulmi kuma zai sanya ido kai tsaye kan yadda shirin hajjin ke tafiya, maimakon dogaro da rahotanni daga wasu mutane.

Farfesa Saleh ya bayyana cewa an yi tanadin tafiya ga mahajjata sama da 70,000 daga cikin 95,000 da aka ba Najeriya damar kaiwa. Ya ce an ɗauki matakan da suka taimaka wajen rage tsadar aikin hajji idan aka kwatanta da shekarun baya. Bugu da ƙari, ana sa ran samun ƙarin sauƙi ga maniyyata a bana domin su samu damar cika wannan rukuni na biyar na addinin Musulunci cikin sauki.

Hukumar ta NAHCON ta kuma bayyana cewa gwamnatin Saudiyya ta fito da wasu sabbin matakan kiwon lafiya da za a bi, inda aka kafa sabbin cibiyoyin kula da lafiya ga mahajjata daga ƙasashe daban-daban. An shawarci hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi su tabbatar da bin waɗannan ƙa’idojin lafiya domin kare lafiyar maniyyata yayin aikin hajji.

A wani ɓangare na shirin hajjin bana, Saleh ya jaddada cewa jagorancin Shettima zai taimaka wajen hana yaɗa bayanai marasa inganci game da hajjin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da mahajjata ke shirin tafiya don gudanar da wannan ibada mai daraja ga duk wani Musulmi mai hali.

By ukarofi