Haka rayuwar shugabanni duniya ta ke bisa muradu da kuma tsarin da kowa ke ganin za ta kai ga ɓullewa a salon mulkin sa. Tun bayan yaƙin duniya na biyu a ka auka wani gagarumin faɗa na cacar baki tsakanin ƙasashen yammacin duniya da tsohuwar tarayyar Sobiyet. Kamar yadda a ka sani yammacin Turai na amfani da tsari na dimokuraɗiyya inda masu bin manufofi na Sobiyet a lokacin ke mulkin gurguzu. Dukkan salon mulkin nan biyu na nan a ƙasashen da a ke gudanar da su ko da kuwa a kan yi zaɓe mai samfurin dimokraɗiyya. In an duba dimokraɗiyya na nufin gwamnatin da jama’a su ka zaba. Gaskiyar magana ba kowane lokaci ba ne a kan samu gwamnatin da jama’a su ka zaba ko ɗan takarar da mutane su ka zubawa ƙuri’a ne ya kan lashe zaɓe a dimokraɗiyya. Gurguzu kuma da kan ɗoru kan tsarin komai na gwamnati ne kan taƙaita kwazon wasu ko kuma ya zama ba lallai ƙoƙarin mutum ua sanya shi fifiko kan wasu ba. A takaice dai mun san labarin yadda maƙarƙashiya ta kawo ƙarshen taraiyar Sobiyet zamanin mulkin Mikha’il Gorbacheɓ. Borris Yeltsin ya yi Turjiya da hakan daga bisani ya sa daular ta rabe zuwa ƙasashe 15 ciki da Rasha kan ta inda Yeltsin ke mulki da kuma Yukrain ta yanzu da a ke taƙaddamar kwance ma ta damara. Haƙiƙa tsayin dakan da a ka samu daga shugaban Rasha mai ci na tsawon zamani Vladimir Putin ya sanya ƙasar cigaba da zama cikin sahun farko na ƙasashen da ka iya girgiza duniya gaba ɗayan ta. Rugujewar taraiyar Sobiyet ba ta hana Rasha mai babban birni a Masko da fadar Kremlin rawar gaban hantsi ba. Nan ma ai wasu ƙasashen mu na Afurka ta yamma da su ka yi bara’a da uwargijiyar su ta mulkin mallaka wato Faransa, ai Rasha su ka nema. Hakanan Rasha da wasu ƙasashe masu tasiri ciki har da Afurka ta kudu sun kafa wata ƙungiya mai suna BRICS da ke da muradin ƙalubalantar mamayar lamuran tsaro da tattalin arziki na yammacin duniya ko ma a takaice a ce Amurka. Har ila yau mun tuna yanda Amurka da Rasha su ka taka rawa a ƙasar Sham kafin faduwar gwamnatin Bashar Al’Asad. Rasha a lokacin na yaƙi don kare gwamnatin Asad inda Amurka ke kare ‘yan gwagwarmayar ƙasar. Bayan wasu lamura sun auku da su ka sauya muradu har ‘yan gwagwarmaya su ka doshi Damaskas, tsohon shugaba Asad ya garzaya sansanin Rasha ne da kuma su ka ba shi kariya ya tashi daga nan zuwa Masko inda ya samu mafakar siyasa. Gudun hijirar da ya yi zuwa Rasha ne ya zama ma sa shiga tudun mun tsira don zai yi wuya ya shiga wata kasa ba tare da samun cikas ɗin zama ko ma a kama shi da ma yiwuwar rasa rayuwar sa ba. Akwai wasu bayanan da ke nuna wasu kura-kurai da Asad ya yi har ya rasa goyon bayan da zai cigaba da zaunar da shi kan mulkin da marigayi mahaifin sa Hafiz Al’Asad ya gadar ma sa. Tamkar dai Sham ta zama fagen gwada ƙarfi tsakanin Amurka da Rasha ne. Wadanna manyan ƙasashen bas a yaƙi da juna kai tsaye sai dai a kaikaice. Babban misali ma ai shi ne yaƙin Yukrain inda Rasha ke son kwance damarar ƙasar biyo bayan neman zama ‘yan ƙungiyar tsaro ta yammacin duniya NATO. Maimakon Amurka ko sauran ƙasashen yamma su tura sojoji don yaƙi da Rasha; sai su ka ɗauki matakin tallafa wa Yukrain da makamai da goyon baya. Hakan ma ya taimaki Yukrain ainun don da zuwa yanzu ƙasar ta miƙa wuya da janye batun NATO. Kuma Rasha yakin a yi ta ta kare ta ke yi ba, manufar ita ce ta wargaza ƙarfin sojan Yukrain don hana ta tasirin zama kishiyar Rasha da taimakon ƙasashen yamma. Alamu dai sun nuna akwai maƙarƙashiyar wargaza tasirin Rasha a duniya don haka zai yi sauki a gama da ita ta hanyar mallakar mubaya’ar ƙasashen makwabta ga ƙungiyar NATO. Da Putin ya yi sako-sako ba shakka da an samu ƙarin ƙasashe da za su shiga NATO su kuma hada kai don wargaza damarar yaƙin Rasha. Putin bai amince da hakan ba don haka ya dau matakin koyawa Yukrain darashi duk da asarar da hakan ya ja wa Rasha. Turai ta sanyawa Rasha takunkumi daban-daban da rike ma ta dukiya don hana ta motsi da kuma ƙarfafa wa Yukrain guiwa ta iya gogaiyar ƙarfi da Rashan. Ba za mu manta yanda jagoran sojan haya na Rasha Yeɓgeny Prigozhin ya ja da Putin inda a ke raɗe-raɗin hallaka shi a ka yi ta hanyar hatsarin jirgin sama bayan an nuna an yafe ma sa kuma komai zai tafi daidai. ƙarfin rundunar sojan hayan ta WAGNER ba kaɗan ba ne wanda ba mamaki ya sa Prigozhin ya ga ya na da ƙarfin cin zarafin Putin da kuma ya manta hakan cin amanar ƙasa ne. Irin waɗannan ƙasashe masu ƙarfin makamai ba sa wargi da duk wanda zai bijire ga muradun ƙasa. Kashe mutum kan zama hanya ta kuɓutar da ‘yancin ƙasa da kare kambun ƙarfin faɗa ajin ta a duniya.
Ba za mu yi mamakin yadda dawowarshugaba Trump mulki a fadar WHITE HOUSE ya ke ɗaukar matakan kusantar Rasha don kawo ƙarshen tsama da ke tsakanin ƙasashen biyu tun da gwamnatin sa na kin jinin yaƙi. A mulkin sa na farko ma ya so ya yi hulɗa da Rasha inda a gefe guda ma har ya zyarci Koriya ta arewa da ke tutiyar mallakar makamin Nukiliya. Tun ganawar sa da shugaba Kim Jon Un a ka samu raguwar zaman cece-kuce daga Koriya ta arewa da ma daina jin labarin gwajin makamai a teku. Akwai masu tunanin Trump zai sa Saudiyya a gaba ba ma lokacin da a ka kashe Jamal Kashoggi a Istanbul inda Trump ya gwale masu wannan tunani ya nuna batun ya shafi harkokin cikin gidan Saudiyya. Yarima Muhammad Bin Salman ya shiga fadar WHITE HOUSE ya gana da Trump da sanya hannu kan yarjejeniyoyin biliyoyin dala. Tsarin Trump shi ne Amurkawa ne ya dace su fi kowa cin gajiyar dukiyar ƙasar su kuma ba daidai ba ne ƙasar ta riƙa tura maƙudan kuɗi waje don ɗaukar nauyin yaƙe-yaƙe. Wani abu ma in kasa na buƙatar kariyar soja ta Amurka za a iya ciniki ta biya sai a tura ma ta sojoji. Tsarin Trump dai na daban ne da ainihin muradun Amurka na tarihi na zama tamkar ‘yar sandan duniya da hakan kan sa ta kashe maƙudan kuɗi da ba da tallafi. Mun ga ai yanda Trump ya dakatar da hukumar raya ƙasashe ta Amurka USAID da ke kashe maƙudan daloli wajen aiyuka daban-daban a sassan duniya.
ƙasar Rasha ta nuna gamsuwa ga taron da jami’an ta su ka gudanar da na Amurka a birnin Riyadh kan yaƙin Yukrain.
Taron dai ya gudana ba tare da gayyatar Yukrain da sauran ƙasashen turai da ke mara baya ga shugaban Yukrain ɓolodymyr Zelenskyy ba.
Alamu na nuna shugaban Amurka Donald Trump na son sulhu da Rasha ta hanyar kawo ƙarshen yaƙin Yukrain.
Kakakin fadar Kremlin a Masko Dimitry Peskoɓ ya ce shugaba Putin ka iya ganawa da Trump a cikin watan nan.
Da alamu taron bai yi wa shugaban Yukrain Zelenskyy daɗi ba don ya ce ba zai yarda da sakamakon taron ba.
Gaskiyar magana matukar Amurka ta samu sulhu da Rasha ba yanda Yukrain za ta iya ɗorewa da yaƙi don ba za ta cigaba da samun makaman da ta ke buƙata wajen fuskantar Rasha ba.
Duk da sauyin manufofin Amurka kan Rasha amma ɓangaren Isra’ila da Falasdinawa na daukar wani salo yayin da jirgin ruwa lode da tallafin boma-bomai daga Amurka ya sauka a Isra’ila bayan amincwa da hakan da shugaba Trump ya yi.
Wannan na zuwa ne yayin da sabon sakataren wajen Amurka Marco Rubio ya isa Isra’ila don ganawa da Firaminista Benjamin Netanyahu da sauran shugabannin ƙasar.
Rubio ya sauka a filin jirgin saman Ben Gurion da ke Tel’aɓiɓ bayan sa’o’i da sako fursunonin Isra’ila 3 da Hamas ta yi.
An so a samu gagarumar tangarɗa a yarjejeniyar tsagaita wuta kan cigaba da sako kamammun Isra’ilawa don Hamas na ganin Isra’ila na jan kafa wajen cimma sharuɗɗan yarjejeniyar.
Rubio ya tattauna da mutan Netanyahu kan muradun Trump a kan Gaza na neman kaurar da Gazawa daga yankin da duk ƙasashen Larabawa su ka yi watsi da matsayar.
An samu bayanan cewa masu shiga tsakani na sulhu da su ka haɗa da Masar da Katar za su gana a birnin Doha don zantawa kan kashi na biyu na yarjejeniyar.
Kammalawa;
Ya kamata shugaba Zelenskyy ya gane an samu sauyin muradu daga Amurka kan Yukrain don haka ya san yadda zai wayance don a samu sulhu. Da alamu in ya yi taurin kai zai iya shiga barazana da ka iya raba shi da mulkin ko ma duniyar gaba daya. ƙasashen turai ba za su ɗore da tallafa wa Yukrain don tinkarar Rasha matuƙar Amurka ta sauya manufa. Zai zama abu mai daɗi duniya ta samu raguwar fitina da maida hankali kan ƙulla ƙawance da ƙarfafa hulɗar arziki.
