Daga AISHA ASAS
Kamar yadda muka ɗauki lokaci muna tattaunawa kan ɓangarorin jiki da ke iya samun matsala a lokutan sanyi, Inda muka soma da fata, zuwa ƙafa da kuma gashi.
A wannan satin, da yardar mai dukka za mu taɓo ɓangaren leɓe, wanda muke fatan mu rufe darasin da shi.
Shi ma leɓe muhimmin waje ne da ke son kulawa ta musamman a lokacin sanyi. Za nu iya cewa, yana daga cikin ɓangarorin jiki da suka fi wahala a lokacin sanyi. Dalili kuwa ababe biyu ne yake buƙata a lokaci ɗaya.
Kamar yadda muka faɗa a darasinmu na bakwanni uku baya, mun sanar da muhimmancin yawaita shan ruwa a lokutan sanyi don samar wa fata lafiya, wanda muka ce na ɗaya daga cikin dalilan da ke sa ta bushewa.
Shi ma a ɓangaren leɓe haka abin yake, domin babbar matsala ce ga ɓangaren rashin wadatattun ruwa a jiki, domin yana haifar da bushewar leɓe, wani lokacin idan abin ya yi ƙamari har da tsagewa, yana jini ko ciwo.
Baya ga ruwa, leɓe na buƙatar mai mai matski akodayaushe. Don haka yana da kyau a dinga yawan shafa man baki a leɓen saboda gudun bushewarsa. Kuma a shawarce ya zama ɗabi’a da’imma shafa man baki duk dare kafin a kwanta. Hakan na ba wa leɓen isashen lokaci da man zai jiƙa shi ba tare da matsala ba.
