Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Babban Limamin Jos, Sheikh Ghazali Ismail Adam ya yi kira ga sauran limamai da malamai da za su gudanar da karatun tafsiri cikin watan azumin Ramadan na wannan shekara da ake gab da farawa, su mayar da hankali wajen faɗakar da al’umma muhimmancin zaman lafiya, haɗin kai da taimakawa juna.
Babban Limamin ya kuma ƙarfafa buƙatar malamai su daina mayar da wuraren tafsiri a matsayin wajen sukar ýan’uwansu malamai, ko faɗar maganganu na ɓatanci da ba su kamata ba, ga wani ɓangare da basa tare da shi a aƙida ko addini.
Babban malamin ya bayyana hakan ne a yayin da yake ƙaddamar da buɗe tafsirinsa na farko a wannan shekara a babban masallacin Jumma’a na Jos. An fara gabatar da tafsirin ne daga farkon Suratul Fatiha sannan aka shiga Suratul Baqara, sura ta biyu a cikin Alƙur’ani mai girma, yayin da Alaramma Malam Hamisu Umar yake ja masa baƙi.
Alƙali Sheikh Ghazali Adam yana tafsirin ne daga fitaccen littafin tafsirin Alƙur’anin nan na ‘Tafsirul Jalalaini’.
Karatun tafsirin ya samu halartar alarammomi da malaman addini da shugabannin al’umma, ciki har da na’ibin Babban Limamin Jos, Sheikh Sharif Nasiru Alfalaqi, da shugaban al’umma kuma Turakin Jos Alhaji Garba Abdulƙadir, da wasu alarammomi da malamai da dama.
