Gwamnatin Tarayya ta aika da sammaci ga kamfanin Multichoice kan ƙarin kuɗi

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

MultiChoice Nigeria na fuskantar tuhuma daga Hukumar FCCPC kan ƙarin kuɗin biyan sabis na DStv da GOtv. Kamfanin ya sanar da cewa daga ranar 1 ga Maris, 2025, za a fara amfani da sabon farashi, inda kuɗin biyan sabis na DStv Premium zai tashi daga Naira 37,000 zuwa Naira 44,500, yayin da Compact+ zai koma Nera 30,000 daga Nera 25,000. Wannan ƙarin kuɗin ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin masu amfani da sabis ɗin.

A sakamakon haka, FCCPC ta buƙaci babban daraktan MultiChoice Nigeria da ya bayyana a gabanta a ranar Alhamis, 27 ga Fabrairu, 2025, domin bayani kan dalilan ƙarin kuɗin. Hukumar ta ce tana duba yiwuwar cin zarafin masu amfani da sabis tare da yunƙurin hana gasa mai kyau a kasuwar sadarwa.

Bugu da ƙari, FCCPC ta ce tana bincike kan yadda MultiChoice ke aiwatar da farashi daban-daban a wasu ƙasashe.

Hukumar ta gargaɗi kamfanin cewa idan ba ta gamsu da bayanin da MultiChoice za ta bayar ba, za ta ɗauki matakan da suka haɗa da hukunci ko takunkumi don kare haƙƙin masu amfani da sabis a Najeriya. FCCPC ta bayyana cewa tana aiki tare da hukumar da ke kula da ɓangaren sadarwa da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki domin tabbatar da adalci a kasuwar talabijin mai biya da sauran ayyukan dijital a ƙasar.

By ukarofi