Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai ba gwamna shawara fanin inganta rayuwar al’umma a karkara, Injiniya Yakubu Nuhu Ɗanja ya faɗi haka a wata hira da manema labarai a Katsina.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sayi kayayyakin abinci da suka haɗa da garin masara, shinkafa da taliya kuma ta rage kashi 10 cikin 100 daga kuɗin abinci domin sauƙaƙa wa al’ummar jihar.
Ya ƙara da cewa za a fara sai da kayan abincin a wurare bakwai da ke shiyyar Daura, Funtua da Katsina,kafin daga bisani a faɗaɗa shirin zuwa sassan jihar.
Injiniya Ɗanja ya kuma sanar da cewa a matakin farko yanzu gwamnati za ta fara saida wa ma’aikatan gwamnati da kuma ma’aikatan da sukayi ritaya.
“Nan ba da jimawa gwamnati za ta duba yiwuwar faɗaɗa shirin ya kai ga sauran al’ummar jihar ” inji Ɗanja”.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙirƙiri wannan shirin na sayen kayayyakin masarufi da saida wa ma’aikatan jihar da marasa ƙarfi domin sauƙaƙa masu halin ƙuncin rayuwa da ake fama.
Ana sa ran mako mai zuwa za a fara sai da kayan abincin a jihar.
