Shigo da mata da matasa cikin harkokin siyasa ne mafita ga Nijeriya — CITAD

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Cibiyar ɓunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma, wato Centre for Information Technology and Development (Citad) ta bayyana muhimmancin shigo da mata da matasa cikin harkokin siyasa musamman a zaɓen 2023, inda ta ce ba kawai matasa su fito kaɗa ƙuri’a ko jagaliyar siyasa ne su ke da rawar takawa ba, a’a, ya zama cewa su ma a zaɓe su a matsayin shugabannin jam’iyyu ko kuma a zaɓi wasunsu su zama shugabanni a zaɓen 2023,

Babban Jami’in shirye-shirye na cibiyar, Isa Garba ne ya bayyana hakan a wata ziyarar haɗin gwiwa da cibiyar ta kai wa jam’iyyun Young People Party (YPP) da kuma People Redamsion Party (PRP) a ofisoshinsu da ke Kano a ranar Lahadin da ta gabata,

Isa Garba ya ƙara da cewa, “Na daga cikin ƙoƙarin da cibiyar ta ke yi wajen wayar da kan mata da matasa domin su shigo a dama da su a harkoki na siyasar ƙasar nan.

“Cibiyar ta gano cewa kaso mafi yawa a cikin al’ummar ƙasar nan mata da matasa ne, kuma dukkanin abubuwan da ake tsarawa ana tsarawa ne ba tare da yawun mafi yawa daga cikin al’umma ba, don haka idan aka samu mata da matasa suka shiga cikin siyasa to zai zama cewa dukkanin matakin da za a ɗauka za a dauke shi ne da yawun al’umma, kuma matsaya ce ta yawun al’umma.”

A na sa jawabin shugaban Jam’iyyar YPP na jihar Kano, Salisu Salisu Usman cewa ya yi haƙiƙa sun yi farin ciki da wannan shiri da CITAD ta bijiro da shi kuma ya kasance an sanya YPP a cikin waɗanda za a yi aikin tare da su,

Yana mai cewa, “Aikin yana da muhimmanci matuƙa ta yadda zai taimaka wajen fitowa da ƴan takarkaru mata da matsa a matakai daban-daban a zaɓe mai zuwa.

“Sannan kuma zai taimaka mana sosai wajen wayar da kai don a guji siyasar dabanci, kana a jawo hankalin matasan su fahimta da siyasar da za ta amfani al’umma”, inji Salisu Usman

Shi ma da ya ke nasa jawabin, shugaban Jam’iyyar PRP na jihar Kano, Comared Sammani Sharif Bashir ya ce PRP ta yi na’am da haɗaka da CITAD ta zo mata da shi, kuma suna goyon baya ɗari bisa ɗari,

Kazalika ya ce, “jam’iyyar PRP na bai wa ƴan takara matasa fifiko fiye da wanda ba matashi ba”.

Ziyarce-ziyarcen dai sun gudana cikin nasara, yayin da baki ya zo ɗaya ga dukkanin shugabannin waɗannan jam’iyyu inda suka yi farin ciki da murna na zaɓo su da CITAD ta yi don aiwatar da wannan aiki tare, sannan suka yi alƙawarin rubuta takardar nuna amincewar yin aiki tare da kuma tabbatar da cewa aikin ya yi nasara kafin zaɓen 2023 mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *