Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hausawa suna da salon rubutunsu na musamman da ake kira ‘Ajami’, rubutun Larabci da aka gyara. Rubuce-rubucen Ajami a ƙasar Hausa an ce sun fara ne tsakanin kashi na ƙarshe na ƙarni na 15 zuwa karni na 16.
Ya fara da ayyukan wasu malamai biyu na ƙasashen waje da suka zo ƙasar Hausa suka zauna.
Na farko shi ne wani masani ɗan ƙasar Morocco, Abdul-Rahman wanda ya rayu kuma ya rasu a Katsina a shekara ta 1520.
A ƙarni na 17 rubutun Larabci/Ajami waɗanda Hausawa na asali suka rubuta sun fara bayyana. Shahararrun malaman Hausa da dama sun rubuta litattafai da waƙoƙi na sharhi, da sauran ayyukan adabi.
Daga cikin waɗannan malamai akwai Muhammad Al-Katshanawi, wanda aka fi sani da Ibn Al-Sabbagh amma an fi saninsa a duk faɗin ƙasar Hausa da sunan Waliyi ɗanmarina.
