Assalam alaikum. Nan gaba kaɗan ne cikin watannan shugabannin ƙasashen duniya za su taru domin tattauna matakan kare ɗumamar yanayi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi da za a gudanar a ƙasar Masar.
Shekara guda bayan da duniya ta fuskanci bala’o’in da ke da alaƙa da sauyin yanayi da ƙaruwar zafin da ba a tava gani ba a tarihin duniya.
Majalisar Ɗinkin Duniya na gudanar da taruka kan sauyin yanayi a kowacce shekara, domin bai wa gwamnatocin duniya damar ɗaukar matakan da suka dace domin rage ƙaruwar ɗumamar yanayi.
Ana yi wa tarukan laƙabi da COPs, wadda a turance ke nufin “Conference of the Parties” wato tarukan ƙasashen duniya waɗanda suka suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MƊD a shekarar 1992.
Taron na bana wanda aka yi wa laƙabi da COP27, shi ne taro na 27 da Majalisar Ɗinkin Duniya ke shiryawa kan sauyin yanayi. Za kuma a gudanar da shi a birnin Sharm el-Sheikh na ƙasar Masar daga ranar 6 zuwa 18 ga watan Nuwamba.
Duniya na qara ɗumama sakamakon ƙaruwar amfani da hayaƙi da ɗan adam ke yi musamman daga hayaƙin da ake ƙonawa saboda amfani da man fetir da iskar gas da kuma ma’adinin Coal.
Yanayin zafin duniya ya qaru da kashi 1.1C kuma ya doshi 1.5C, kamar yadda masana kimiyyar sauyin yanayi na MƊD, da kuma Majalisar gwamnatocin duniya kan sauyin yanayi (IPCC) suka bayyana.
Idan zafin duniya ya ƙaru da kashi 1.7 zuwa 1.8. IPCC ta yi hasashen cewa rabin al’umar duniya za su fuskanci barazar ci gaba da rayuwa saboda tsananin zafi da raguwar kaɗawar iska.
Domin kare afkuwar hakan, ƙasashe 194 sun rattava hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris a 2015, tare da alƙawarta haɗa hannu domin hana zafin duniya ƙaruwa da kashi 1.5C.
An gayyaci gwamnatocin ƙasashe fiye da 200.
To sai dai wasu shugabannin manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ciki har da shugaban Rasha Vladimir Putin ba za su halarci taron ba. To amma ana sa ran halartar wakilai daga ƙasar.
Haka kuma wasu ƙasashen ciki har da China kawo yanzu ba su tabbatar da cewa ko shugabanninsu za su halarci taron ba.
Mai masaukin baƙi ƙasar Masar ta yi kira ga ƙasashen duniya da su ajiye bambancin ra’ayi da na siyasa da ke tsakaninsu a gefe guda su kuma nuna ‘halin dattako’.
An sa ran kuma ƙungiyoyin kare muhalli, da ƙungiyoyin al’umma, da na ‘yan kasuwa da na addinai su ma za su halarci taron.
Wannan shi ne karo na biyar da ake gudanar da taron sauyin yanayi na COP a nahiyar Afirka.
Yankin da gwamnatocin duniya suka yi amanna cewa zai ja hankalin ƙasashen duniya sakamakon mummunar illar da sauyin yanayi ya yi wa nahiyar. IPCC ta ce nahiyar Afirka ɗaya ce daga cikin ɓangarorin duniya da sauyin yanayi ya yi wa illa.
A halin yanzu, an yi ƙiyasin cewa mutum miliyan 17 ne ke fuskantar ƙarancin abinci a yankin gabashin Afirka saboda matsalar fari.
To amma, zaɓar Masar a matsayin wurin da za a yi taron ya janyo cece-kuce.
Wasu masu rajin kare ‘yancin ɗan adam da masu rajin kare muhalli na cewa gwamnatin Masar ta hana su halartar taron saboda yadda suke sukar ƙasar game da yadda ta ke tafiyar da al’amuran ‘yancin dan adam.
Kuɗi shi ne babbar matsalar da ke damun taron sauyin yanayi.
A shekarar 2009, manyan ƙasashe masu arziki sun ce za su samar da kuɗi dala biliyan 100 zuwa shekarar 2020, ga ƙasashe masu tasowa domin taimaka musu rage gurɓataccen hayaƙi domin fuskantar dumamar yanayi.
To amma an kasa cimma wannan muradi, inda aka mai da shi zuwa shekarar 2023.
Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA, 08168716583.
