ASUU na shirin zanga-zanga kan ƙin biyan mambobinta cikakken albashi

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Akwai yiwuwar ɗaliban jami’oin Nijeriya su sake fuskantar rashin malamai a cikin aji sakamakon shirin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) na hana malamai shiga aji na yi ɗaya a matsayin zanga-zangar nuna rashin jin daɗi kan matakin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka na “babu aiki, babu albashi” a kan malaman.

Rahotanni sun ce, ASUU za ta shirya zanga-zangar ne a rassanta da ke jami’o’in gwamnati a faɗin ƙasa.

An ce mambobin ASUU za su yi zanga-zangar ne ta hanyar ƙin shiga azuzuwa balle kuma su karantar da ɗalibai.

Ɗaya daga cikin shugannin ASUU na ƙasa ne ya tabbatar wa jaridar Intelregion da hakan yayin tattaunawa da wakilinta ranar Lahadi.

Idan za a iya tunawa, a ranar Juma’a 16, ga Oktoban 2022 ASUU ta janye yajin aikin da ta yi bayan rufe jami’o’i na tsawon wata takwas inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka cim ma shekaru da suka gabata.

Yayin yajin aikin ne gwamnati ta ce ba za ta biya malaman watannin da suka shafe ba su yi aiki ba, lamarin da ASUU ta ce ba zai saɓu ba.

Sai dai kuma, duk da ASUU ta janye yajin aikin nata, mambobinta sun yi iƙirarin rabin albashi aka biya su a watan Oktoba, yayin da gwamnati ta ce cikakken albashi ta biya su a watan kamar yadda Ma’aikatar Ƙwadago ta yi iƙirari.

Bayan taron da shugabannin ASUU na ƙasa suka yi ran 8 ga Nuwamba, 2022, jagororin ƙungiyar sun ce ba za su sake tsunduma wani yajin aikin ba amma za su yi amfani da wasu hanyoyi da matakai na daban wajen neman haƙƙinsu a hannun gwamnati.

“Za mu yi zanga-zanga. Kowane reshe na ƙungiyar zai zaɓi ranar da ya dace masa, akwai buƙatar gwamnati ta fahimci cewa mu ba ma’aikatan wucin-gadi ba ne,” in ji wata majiyya daga ASUU.

By Editor