
Daga BELLO A. BABAJI
Yayin da al’umma ke fuskantar tsadar rayuwa a ƙasar, Sanata Orji Kalu ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sane da halin matsin da ake fama da shi a ƙasar kasancewar ya kan kewaya cikin dare don gani da idonsa tare da ɗaukar matakan daidaita al’amuran taɓarɓarewar harkar tattali.
Hauhawar farashi ya ƙaru da kaso 32.7 a watan Satumba, 2024 kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasa, NBS ta bayyana.
Tun lokacin da aka cire tallafin man fetur da rugujewar darajar Naira ne kayayyaki suka ta yin tashin gwaoron zabi.
Sanata Kalu ya ce ba sabon abu ba ne ga Nijeriya hakan da ke faruwa, inda ya ce har yanzu ƙasar ta na kan farfaɗowa daga matsalolin da annobar COVID-19 ta haifar.
Ɗan majalisar ya ƙara da cewa Naira 14m ake ba su a wata ba ta isar sa sayan man fetur ɗin da zai kai shi mazaɓarsa da kula da aikin ofishinsa.
Har’ilayau, Sanata Kalu ya musa batun cewa an bai wa kowane ɗan majalisa motar alfarma, inda ya ce kaɗai an yi hakan ne wa jagororin kwamitocin Majalisar.
