Ɗalibai sun ƙone gidan shugaban makaranta kan zaftare N23m a Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wasu fusatattun ɗalibai da ke makarantar Kwalejin kiwon lafiya ta Jega a Jihar Kebbi sun ƙona gidan Shugaban Kwalejin, Haruna Sa’idu Sauwa da farfasa motarsa.

Ɗaliban sun fara zanga-zangar ne bayan samun batun zargin hukumar gudanarwa ta makarantar na karɓe wasu maƙudan kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira miliyan 23 daga hannun ɗalibai 250 da ke shirin kammala karatu.

Wata majiya ta ce lamarin ya samo asali ne daga wata sabuwar tsangaya da aka ƙirƙiro (Public health) wadda da farko an dangana ta ne da wani sashi da kuma Ƙungiyar Lafiyar Al’umma ta Ƙasa.

Kwalejin ta haɗe sabon ɓangaren ne da tsangayar Tsaftace Muhalli inda ta buƙaci karin Naira 65,000 daga kowane ɗalibi baya Naira 30,000 da kowannen su ya biya da fari.

Sakamakon zargin hukumar gudanarwar da wawure kuɗaɗen ne, sai ɗaliban suka yi ta jefe-jefen motoci da sanya wuta a gidan shugaban makarantar gabannin jami’an tsaro su hallara.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Nafi’u Abubakar ya ce za su sanar cikakken bayanai game da lamarin da zarar sun kammala bincike.

Kawo yanzu dai, karatu a kwalejin ya shiga halin tsaka-mai-wuya kasancewar aukuwar al’amarin wanda ya yi sanadiyyar dakatar da ayyuka da dama.

By Babaji